Ajiya maganin watarana: Dan Najeriya ya fasa asusunsa, kudin da ya tara sun girgiza intanet
- Wani dan Najeriya ya fasa asusunsa tare da bayyana makudan kudaden da ya tara a ciki wanda mutane da dama suka nuna mamakinsu
- Mutumin dai bai bayyana lokacin da ya fara jefa kudi a asusun ba, amma wani faifan bidiyo ya nuna shi yana kirga guminsa abin sha'awa
- Bidiyon ya ja hankalin jama'a sosai a shafukan intanet, inda mutane da yawa ke cewa wanda ke da kudi ne kadai zai iya ajiye wani abu don gaba a irin wannan lokaci
Ya zuwa yanzu dai, wani dan Najeriya ya fasa asusunsa don gane wa idonsa makudan kudaden da ya tara a ciki.
Ko da yake bai bayyana lokacin da ya fara tara kudin ba, wani faifan bidiyo ya nuna mutumin yana kirga kudinsa masu daraja daban-daban.
Ajiye kudi sai mai arziki
Kokarin da mutumin ya yi na tara wani kaso daga kudinsa na shiga saboda ya mora a nan gaba ya ja hankalin jama'a a shafukan sada zumunta. Mutane da yawa sun yaba masa saboda kokarin da ya yi ganin yadda ake fama da babu a kasar nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Duk da haka, wasu da yawa da suka yi martani sun nace cewa mutum zai iya ajiye irin wadannan kudaden ne kawai idan dama yana da kudi. @gossipmillnaija ne ya yada bidiyon a shafin Instagram.
Kalli bidiyon:
Martanin 'yan sohiyal midiya
Bidiyon ya jawo muhawara kafar sada zumunta ta Instagram. Ga kadan daga cikin abubuwan da mutane ke cewa:
@commedian_eddyranking:
"Bayan na yi ajiya na 1yr + na bude nawa watara na ga 2500 na ga wadanda suke amfani da tsafi a akwatinsu."
@omorewa_beautyempire:
"Wannan mutumin dai bai da budurwar da za ta dame shi da banibani!! Babu mata babu matsala."
@nba__savage_ :
"Wannan mutumin zai iya ceto Najeriya."
@mayorjnr_:
"Ba sai mutumin da ya ga kudi ne zai iya ajiya ba."
@toviaogun:
"Ya yi kyau, da fatan ba zai kashewa wata budurwa ba ko."
@austin_mulla__:
"Ina ganin irin wannan ajiya a matsayin asara... Kudin da ya kamata ka yi amfani dasu ne fa, kawai ka dage lokacin amfani dasu ne... duk daya ne dan uwa."
Zai shilla Amurka: Yaron da ya kwaikwayi gadar sama ta Kano ya samu 'Scholarship'
A wani labarin, hazakar wani yaro ta zama silar ingantuwar rayuwar iyalansa yayin da wani kamfanin gine-gine ya ga kyakkyawan aikinsa.
Yaron dan Najeriya mai suna Musa Sani ya ba mutane sha'awa a yanar gizo bayan da ya gina wani kwafin gadar sama ta jihar Kano da ya gina da tarkacen wasan yara.
Wani dan Najeriya mai suna Aminu Adamu Abdullahi da yada hotunan Musa da kirkirarsa a Facebook, ya bayyana cewa wani kamfanin gine-gine mai suna Ronchss Global Resources, ya baiwa Musa tallafin gurbin karatu a jami’ar kasar Amurka.
Dambe Ya Kaure Tsakanin Ango Da Wani Mutum Da Ya Lika Masa Kudi a Wajen Shagalin Bikinsa, Bidiyon Ya Yadu
Asali: Legit.ng