'Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Mutane 14 a Masallaci a Kaduna, Sun Kuma Sace Mata Da Dabobbi
- Wasu miyagun yan bindiga da sun kai hari kauyuka a karamar hukumar Giwa ta Kaduna sun sace mutane 14 a masallaci a ranar Alhamis
- Wasu mutane mazauna garin sun tabbatar da harin sun ce yan bindigan sun raba kansu, wasu na masallaci wasu kuma sun bi gidaje sun sace mata da dabobi
- Majiyoyin sun bayyana cewa a zuwa ranar Juma'a mutane hudu cikin wadanda yan bindigan suka sace sun samu 'yancin kai sun dawo gida
Jihar Kaduna - An sace wasu masallata a yayin da yan bindiga suka kai hari a masallaci a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Wasu majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa yan bindigan sun kai harin ne lokacin da mutanen ke sallar Ishai a ranar Alhamis.
Mutanen garin sun tabbatarda harin, sun magantu kan barnar da yan bindigan suka yi
Majiyar da ke zaune garin ya ce:
"Sun zagaye masallacin suka sace mutane 14. Sun kuma sace shanu da ba a san adadin su ba daga kauyen Tudun Amada duk a Giwa."
Daily Trust ta gano cewa yan bindigan sun dade suna kokarin kai hari a jihar amma yan sakai suna hana su shiga garin.
Da ya ke magana a kan harin, wani mazaunin garin daban ya ce:
"Yan bindigan sun raba kansu, wasu suna masallaci, wasu kuma suka rika bi gida-gida suka sace fiye da mata goma.
"Wasu daga cikinsu kuma suna can suna sace dabobin gida kamar shanu, tumaki da akuyoyi da suka haura daruruwa."
Wakilin majiyar Legit.ng ya ce a yau Juma'a an sako kimanin mutum hudu cikin wadanda aka yi garkuwa da su.
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce zai bincike sannan zai bada bayani, bai bada bayanin ba har lokacin hada wannan rahoton.
'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto
A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.
An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.
Asali: Legit.ng