Mai Mala bai bani wata wasika ba: Gwamna Neja ya yi martani mai zafi
- Bangaren Gwamnan Neja Abu Lolo sun yi martani game da wasikar da aka saki na Mai Mala Buni
- Gwamna Abu wanda yanzu shine mukaddashin shugaban APC yace shi Mai Mala bai bashi wata wasika ba
- Hadiman Mai Mala sun jaddawa cewa maigidansu ba korarsa aka yi ba, da kansa ya mika mulki
Mukaddashin Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Abubakar Sani Bello ya karyata rahoton cewa ya karbi wata wasika daga hannun gwamnan Yobe, Mai Mala Buni.
Sani Bello, wanda yayi martani kan labarin cewa Mai Mala ya bashi wakilcin shugabancin jam'iyyar saboda zai tafi Dubai jinya, ya bayyanawa manema labarai cewa shi dai bai ga wata wasika ba, rahoton TheNation.
Wannan ya ci karo da wasikar da hadiman Mai Mala ke yadawa a kafafen sada zumunta cewa ba tsige maigidansu aka yi ba.
Yayinda aka tambayesa kan lamarin wasikan Gwamna Sani Bello yace:
"Ni ban ga wata wasika ba."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A riwayar Vanguard,Wani hadimin gwamnan ya kara haske inda yace:
"Buni da farko Sakataren jam'iyyar, Akpanudoedehe, ya baiwa rikon kwarya amma a ranar Litinin da ya ga yadda ake goyon bayan Gwamna Bello yayi masa juyin mulki, sai Buni yayi gaggawan rubuta wata wasikar na mikawa Bello wakilci."
"Saboda haka shur-shure ne, kuma shi yasa suka mayar da ranar watar rubuta wasikar baya, sun kasa aiko mana da wasikar saboda mun san abinda ke ciki da kuma dalilin da ya sa suka rubuta."
Mun kawo rahoton hadiman Mai Mala sun bayyana cewa maigidansa ba korarsa aka yi ba, da kansa ya mika mulkin jamiyyar hannun Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, kafin tafiya jinya kasar Dubai.
Wani sashen wasikar mai dauke da kwanar watan 28 ga Febrairu tace:
"Ina mai sanar da kai cewa zan tafi neman lafiya kasar UAE daga Yau, 28 ga Febrairu, 2022."
"Saboda haka, na wakilta ayyukan ofishina na Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar nan gare ka."
"Ina kira ga mambobi su hada kai da Gwamna Abubakar Sani Bello ta hanyar bashi goyon baya kamar yadda kuka bani."
Jawabin El-Rufa'i
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ba zai taba komawa kujerar Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana hakan.
A hirar da yayi a shirin Politics Today, El-Rufa'i ya ce Buni ko ya dawo an fitittikeshi daga kujerar gaba daya har abada.
Ya ce Shugaba Buhari da gwamnonin APC 19 sun yi ittifaki kan cire Mai Mala Buni.
El-Rufa'i yace:
"Buni ya tafi har abada, Sakatare ya tafi. Gwamna Bello ne kan kan kujerar yanzu kuma Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnoni 19 na bayansa. Buni ko ya dawo zai dawo ne a matsayin Gwamnan Yobe amma ba Shugaban jam'iyyarmu ba."
"Shugaba Buhari ya bada umurnin cireshi. Buni da mutanensa sun samu wata doka daga kotu na hana taron gangami amma ya boye."
"Ban san dalilin da zai sa mutum yayi irin haka ba."
Asali: Legit.ng