Harin Kebbi: 'Yan ta'adda sun halaka sojoji 18, 2 sun yi batan dabo, Rundunar sojin Najeriya
- Rundunar sojin Najeriya ta sanar da halakar sojoji 18, jigatar wasu guda takwas da kuma batan wasu biyu a harin Kebbi
- A yammacin Talata ne 'yan ta'adda suka tare tawagar mataimakin gwamnan Kebbi tare da kwamandan sojoji a yankin Kanya da ke Danko Wasagu
- Daga cikin makaman da 'yan ta'addan suka tsere da su akwai: konanniyar motar yaki 1, bindigar AA Dushka guda 1 da AK-47 guda 18
Kebbi - Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan sojoji goma sha takwas, jigatar sojoji takwas da kuma mutuwar biyu a farmakin da 'yan ta'adda a yankin Kanya da ke karamar Danko Wasagu ta jihar Kebbi wanda ya auku a ranar Talata da yammaci.
Premium Times ta ruwaito cewa harin ya ritsa da mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Samaila Yombe tare da kwamandan rundunar soji da ke Kebbi yayin da suka kai ziyara yankin.
Majiyoyi sun sanar da cewa sojoji 13 suka rasa rayukansu yayin farmaki. Amma majiya daga hedkwatar tsaro ta tabbatar da cewa sojoji goma sha takwas aka rasa a artabun.
Sojojin da lamarin ya ritsa da su sun hada da na bataliya ta 223 ne da ke zama a Zuru, jihar Kebbi, Premium Times ta ruwaito.
Kamara yadda rahoton ya bayyana, akwai wasu daga cikin sojojin tawaga ta goma daga bataliyar.
"Dakarun sojin sun yi arbatu da 'yan ta'adda amma 'yan ta'addan sun fi su yawa. Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai sojoji goma sha takwas, sojoji takwas sun jigata yayin da har yanzu ba a ga wasu biyun ba. Kayayyakin da 'yan ta'addan suka tsere da su sun hada da konanniyar motar yaki 1, bindigar AA Dushka guda 1, AK-47 18," takardar tace.
Takardar ta kara da bayyana cewa har yanzu sojojin Najeriyan ba su saduda ba kuma suna nan da karsashinsu na yakar ta'addanci.
Bayan kalmashe N26m, 'yan ta'adda sun sako dagaci da wasu mutum 35 a Katsina
A wani labari na daban, masu garkuwa da mutane sun sako dagaci da sauran mutane 35, bayan biyan N26 miliyan a matsayin kudin fansa, bayan wadanda aka yi garkuwan dasu sun kwashe kwana 29 a hannun 'yan bindigan kafin su sake su a yammacin Lahadi.
'Yan bindiga sun sako dagacin Guga cikin karamar hukumar Bakorin jihar Katsina, Alhaji Umar da sauran mazauna kauyen guda 35 bayan amsar N26 miliyan a matsayin kudin fansa.
Premium Times ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka shiga kauyen a ranar 7 ga watan Fabrairu, inda suka halaka mazauna yankin guda 10 daga bisani suka yi awon gaba da mutane 36, duk da dagacin kauyen.
Asali: Legit.ng