Yin arziki 'yan Crypto zai tabbata: Amurka ta juyo kan 'yan Crypto, za su ga canji nan kusa
- Wata sabuwa odar zartarwa wacce Shugaba Joe Biden ya sanya wa hannu ta ba da cikakken hasken sauyin rayuwa ga 'yan crypto a Amurka
- Odar ta zartarwa ta yi kira ga hukumomin gwamnati a Amurka da su dauki matsaya daya kan crypto da sauran kadarorin intanet
- An sami rahotannin cece-kuce a fadar White House tsakanin ma'aikatar kudi da jami'an fadar White House game da shirin aiwatar da wannan manufa
Joe Biden, shugaban kasar Amurka ya nuna alamar wani yunkuri na kafa tarihi a kasuwancin crypto a Amurka da ma duniya baki daya, matakin da masana suka yi hasashen zai kawo sauyi a duniyar crypto.
An ce hakan zai kawo sauyi ne a cikin tsari mai tsawo da ake ta tsammani, wanda ya zama damuwa a duniyar crypto, yawanci saboda al'amurran da suka shafi ka'idojin kudi a duniya kasancewar ana ganin crypto a matsayin sabon nau'in kudi, a cewar wani rahoto na CNBC.
Nesa ta zo kusa
An samu labarin rashin fahimta a fadar shugabancin Amurka ta White House tsakanin jami'ai da sakatariyar baitulmalin kasar, Janet Yellen wanda hakan ya haifar da koma baya wajen tabbatar lamarin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya zuwa yanzu dai an samu abubuwa sun fara daidaita, domin kuwa bayanai game yiwuwar tabbatar da okar zartarwar za ta kankama bayan sanya hannu.
A karshe Shugaba Biden ya sanya hannu kan hakan a ranar Laraba, 9 ga Maris, 2022, yana mai kira ga hukumomi da su dauki hanyar da ta dace ta doka da sa ido kan kudaden intanet, in ji wata takarda daga fadar White House.
Abin da ya kamata ku sani game da lamarin
Lamarin dai zai mayar da hankali kan manyan fannoni guda shida: Kariyar kwastomomi da masu saka hannun jari, wadatar kudi, dakile haramtaccen ciniki da ayyuka munana, gogayyar Amurka a fagen a fadin duniya, hada-hadar kudi da kirkira mai ma'ana.
Kange masu siye daga hadari da zamba shine muhimmin sashi na tsarin. Mutane da yawa sun tafka faduwa a kasuwar crypto, hakazalikan an damfare su, kana sun yi asarar makudan kudade ta hanyar kutse 'yan tsatsuba.
Dare daya: Yadda dan crypto ya zama miloniya a wata sabuwar duniyar crypto wai ita NFT
A wani labarin, Daniel Maegaard a da yana samun Naira 6,500 kacal a kowane awa idan ya yi aiki a wani gidan mai a karshen mako yayin da yake karatun ilimin halayyar dan adam a wata Jami'ar.
Maegaard ya kasance yana tara kwabban crypto yayin da yake hada aikinsa da karatu amma gogewa a fannin fasaha da sa'ar rayuwa sun sa ya zama hamshakin attajirin dare daya.
Ya yi tuntube da wani tsagin duniyar crypto da ake kira Non Fungible Tokens (NFTs) shekaru kafin su zama abin da suke yanzu. Wannan ya ba shi damar zama miloniya a cikin shekaru goma da suka gabata.
Asali: Legit.ng