Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, sun yi awon gaba da mata
- Yan ta'adda da safiyar Alhamis, sun sake kai wani hari kauyen karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna
- Rahoto ya tabbatar da cewa maharan sun kashe akalla mutum uku a Anguwar Galadima, sun yi awon gaba da wasu mata biyu
- Wani mazaunin yankin ya ce sun jiyo karar harbin bindiga na tashi, kuma maharan sun aikata ta'addancin su ba tare da turjiya ba
Kaduna - Yan bindiga da yawan gaske sun farmaki wani layi a Anguwan Galadima, kauyen Gonin Gora, karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yan ta'addan sun halaka mutane uku, kuma suka yi awon gaba da mata biyu yayin harin.
Shugaban ƙungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab, shi ya bayyana haka ranar Alhamis, 10 ga watan Maris, 2022.
Ya ce yan ta'addan sun farmaki mutanen yankin da sanyin safiyar Alhamis ɗin nan, kuma sai da suka shafe aƙalla awa ɗaya suna aikata ta'addancin su kan mutane.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
The Nation ta rahoto Rabaran Hayab ya ce:
"Mutanen da yan bindigan suka kashe sune Aminu Bage da kuma ɗansa, sai kuma wani makocinsa da lamarin ya rutsa da shi.."
Haka nan, wani mazaunin yankin ya bayyana cewa sun ji ƙarar harbe-harbe a yankin da lamarin ya faru.
"Mun ji ƙarar harbe-harben bindiga ya mamaye ilahirin yankin da abun ya auku, yan ta'addan sun aikata abin da ya kai su ba tare da samun turjiya ba kuma suka tafi da mutane."
"A halin yanzun yan bindiga sukan kashe mutanen da suka yi garkuwa da su, da nufin jefa tsoro a zukatan al'umma."
Har zuwa yanzun, hukumomi a jihar Kaduna ba su ce komai ba game da wannan sabon harin da yan bindiga suka kai.
A wani labarin kuma mataimakin gwamnan Kebbi ya tsallake rijiya da baya yayin da yan bindiga suka buɗe wa tawagarsa wuta a wurin jaje
Yan bindiga sun farmaki tawagar motocin mataimakin gwamnan jihar Kebbi yayin da yaje ta'aziyyar kashe mutane a Kanya.
Rahoto ya nuna cewa jami'an tsaron dake tare da shi sun yi batakashi da maharan, kuma ɗan sanda mai mukamin ASP ya rasu.
Asali: Legit.ng