An damke wanda ake zargi da kisan tsohon jami'in Soja da dogarinsa a Kaduna
- Bayan watanni hudu, an damke daya daga cikin wadanda suka bi tsohon Soja gida suka hallakashi
- A watan Nuwamba 2021 wasu yan bindiga suka kai hari unguwar Rigasa inda suka kashe AVM Maisaka da dogarinsa
- Uwargidar marigayin, Hajiya Fatima Maisaka, ta bayyana cewa basu dauki komai daga gidan ba
Kaduna - Hukumar yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta damke wani Mohammed Giwa, wanda ake zargi da kisan marigayi Muhammad Maisaka, tsohon jami'in Soja sama.
Giwa na cikin yan bindiga 200 da hukumar yan sanda ta bayyanawa duniya ranar Laraba.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ya bayyana cewa sun kwato bindigogin AK47 guda 18, harsasai 2,000, loda ka harba 11, kananan bindigogin gargajiya 10, dss.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar 9 ga Nuwamba, 2021 wasu tsagerun yan bindiga sun hallaka wani tsohon Sojan sama, Air Vice Marshal, Mohammed Maisaka, a gidansa dake unguwar Rigasa a jihar Kaduna.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa
Wani mazaunin unguwar da Legit Hausa ta tuntuba ya bayyana cewa yan bindiga sun bindigeshi tare da dogarinsa, Mohammed Musa.
An tattaro cewa yan bindigan sun dira gidan da daren Litnin misalin karfe 8:30 na dare kuma suka harbesu har lahira.
Uwargidar marigayin, Hajiya Fatima Maisaka, ta bayyana cewa basu dauki komai daga gidan ba
Malam Bashir Bamalli, wanda makwabcin marigayin ne ya bayyana mana yadda abin ya faru.
Yace:
"A gida suka harbeshi da dogarinshi, mutum biyu kawai aka kashe. Shine mai asibitin MSK."
"Kafin yayi ritaya shine shugaban asibitin Airforce. Ba masu garkuwa da mutane bane, kawai kasheshi suka zo yi."
Tuni ba shi da lafiya, bai dade da dawowa ba
Bashir ya kara da cewa can dama bai da lafiya kuma bai dade da dawowa ba daga kasar Indiya inda yaje jinya.
"Bai da lafiya ma, bai dade da dawowa ba daga Indiya, saboda haka bamu san abinda yayi musu ba amma bincike zai bayyana gaskiya," ya kara
Asali: Legit.ng