Da Duminsa: Tankan Man Fetur Ta Kama Da Wuta a Gidan Mai a Legas

Da Duminsa: Tankan Man Fetur Ta Kama Da Wuta a Gidan Mai a Legas

  • Wata tankar dakon man fetur ta kama da wuta a yayin da ta ke sauke fetur a wani gidan mai a Legas
  • Wutan da ya tashi ya shiga wani gida mai bene uku inda ya kone dakuna da dama hakan ya janyo asarar dukiyoyi
  • Hukumar bada agajin gaggawa na kasa, NEMA, da jami'an hukumar kwana-kwana na Legas sun isa wurin sun bada dauki

Legas - Jami'an Kwana-kwana suna can suna kokarin kashe wuta da ta kama wani gini mai bena uku a unguwar Mushin a Legas bayan wani tanka dauke da man fetur ta kama da wuta a kusa da gidan mai.

Daily Trust ta gano cewa tankar tana sauke man fetur ne a gidan man misalin karfe 1 na rana, nan take kawai ta kama da wuta kuma wutan ya shafi wani gida da ke kusa.

Kara karanta wannan

Kisan Kebbi: 'Yan majalisa sun roki FG ta tura sojojin sama da kasa domin ragargazar 'yan bindiga

Da Duminsa: Tankan Man Fetur Ta Kama Da Wuta a Gidan Mai a Legas
Tankan Man Fetur Ta Kama Da Wuta a Gidan Mai a Legas. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shugaban hukumar bada tallafin gaggawa na kasa, NEMA, reshen jihar Legas, Ibrahim Farinloye, ya ce ba a rasa rai ba.

Ya ce:

"Gobara ta tashi ne sakamakon fashewar tankan man fetur da ke kokarin sauke mai misalin karfe 1 na rana kuma wutan ya bazu zuwa wani gida mai bene uku da ke kallon ofishin yan sanda na Mushin Legas.
"Ba bu wanda ya rasa ransa ko ya yi rauni. An yi nasarar kashe wutan. Ana can ana kokarin ceto benen kada wutan ya kona shi baki daya. An ceto kayayyaki kadan."

Hukumar kwana-kwana da bada taimakon gaggawa ta Legas ta magantu kan gobarar

Hakazalika, Hukumar Kwana-Kwana ta Jihar Legas ta ce ta tura jami'anta zuwa wurin da abin ya faru don kashe wutan.

Kara karanta wannan

Wani Bawan Allah Mai Shekaru 36 Ya Faɗa Rijiya Ya Mutu a Kano

Shugaban hukumar, Mrs Adeseye Margaret, cikin sanarwar binciken farko ta ce tanka mai dauke da fetur lita 33,000 ne ta kama da wuta.

Ta ce tankar tana son 'juye man fetur ne a gidan man.

"Duk da cewa ba a kammala gano ainihin abin da ya janyo tashin wutar ba, hukumar kwana-kwana ta Legas tana bada gudunmawar da ta dace kuma za ta fitar da bayani.
"Ana shawartar masu ababen hawa sun guji bin hanyar Idi Oro Corridor na Agege Motor Road," ta kara da cewa.

Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira

A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.

An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.

Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: