Karin bayani: 'Yan sanda sun mutu yayin da motar tawagar ministocin Buhari ta yi hadari
- Daya daga cikin motocin da ke cikin ayarin shugaban ma’aikatan Buhari, Ibrahim Gambari, da minista Fashola da takwaransa Ngige sun yi hatsari a Asaba, jihar Delta
- ‘Yan sanda hudu ne ake fargabar sun mutu a hatsarin wanda aka ce ya faru ne da yammacin ranar Talata, 8 ga watan Maris
- Rahotanni sun ce manyan jami’an gwamnatin sun je babban birnin jihar Delta ne domin duba wata gada da aka gina
Asaba, jihar Delta - Ayarin shugaban ma'aikata, Ibrahim Gambari; Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; da takwaransa na ma'aikatar kwadago da samar da aikin yi, Christ Ngige, sun yi hatsari a yammacin ranar Talata, 8 ga watan Maris
Jaridar Punch ta ruwaito cewa hatsarin ya afku ne a yayin duba wata gada a garin Asaba na jihar Delta, inda rahoton ya kara da cewa ‘yan sanda hudu ne ake fargabar sun mutu.
An tattaro cewa direban motar ne ya rude yayin tuka motar da ke dauke da jami’an tsaro inda ta fada cikin wani rami mai zurfi.
Shaidun gani da ido sun bayyana yadda lamarin ya faru
Wani shaidan gani da ido, John Okorie, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da motar da ke dauke da wadanda lamarin ya rutsa dasu ke tattaunawa kan kwanar da ta kai ga wajen aikin gina gadar Neja ta biyu a Asaba.
An tattaro cewa motar ‘yan sandan ta yi gudu ne don haduwa da sauran tawagar motocin ministocin ne a lokacin da ta kauce daga titi kuma ta yi hatsari.
Har ila yau, wani direba a Delta, wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce:
“Lamarin ya yi muni matuka.
“Direba dan sandan yana gudu yayin da ake tattaunawa kan lankwasar hanyar wanda saboda gudun ya kasa sarrafa motar. Suka fada cikin wani rami mai zurfi. Ni ina bin bayan ayarin, ina tuki na a hankali.
“Da taimakon wasu mutane mun ceto hudu daga cikinsu amma sun samu munanan raunuka. Suna ta ihu yayin da motar ta fado musu.”
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya ce har yanzu bai samu rahoton faruwar hatsarin ba.
Yan bindiga sun kai wa Mataimakin Gwamna hari a kan hanya
A wani labarin, tsagerun yan bindiga sun farmaki jerin gwanon motocin mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Samaila Yombe, ranar Talata da daddare.
Vanguard ta tattaro cewa yan ta'addan sun kai wa tawagar mataimakin gwamnan hari ne tsakiyar kauyen Kanya da misalin karfe 8:00 na dare.
A cewar sakataren watsa labarai na mataimakin gwamnan, Abdullahi Yalmo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami'in ɗan sanda ASP Idris Umar Libata, ya rasa rayuwarsa.
Asali: Legit.ng