Muhimman abubuwa 5 da ya dace a sani game da marigayi DIG Egbunike

Muhimman abubuwa 5 da ya dace a sani game da marigayi DIG Egbunike

A safiyar ranar Laraba ne labarin rasuwar DIG Joseph Egbunike ta riski rundunar 'yan sandan Najeriya.

An ruwaito yadda ya rasu ranar Talata, minti 10 bayan duba shi a asibiti a Abuja.

Ga abubuwa guda biyar da ya kamata ku sani game da marigayin DIG.

Muhimman abubuwa 5 da ya dace a sani game da marigayi DIG Egbunike
Muhimman abubuwa 5 da ya dace a sani game da marigayi DIG Egbunike. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Shugaban FCIID

An haifi Joseph Obiajulu Egbunike a Anambra, kuma shine mataimakin sifeta janar na 'yan sanda wanda dake da alhakin kula da sashin binciken sirri na rundunar a lokacin rayuwarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban tawagar bincike akan lamarin Kyari

Sifeta janar na 'yan sanda, Usman Alkali Baba ya nada Egbunike a matsayin shugaban tawagar bincike akan zargin dakataccen DCP Abba Kyari da hannu a damfar $1.1 miliyan da ya hada da garwurtaccen dan damfarar yanar gizo, Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Jami’in ‘Dan Sandan da ya yi bincike kan Abba Kyari ya mutu kwatsam a ofis

Ya karanta fannin akawunci

Yayi digirin shi na farko a fannin kirga da ajiyar kudi a jamiar Najeriya ta Nsukka, haka zalika, ya karanci fannin shari'a a digirin shi na biyu a MILD, sannan ya karanta fannin tuhumar masu laifuka a digirin sa na uku.

Ya yi aiki a NNPC

A lokacin bautar kasar da yayi, Egbunike yayi aiki a matsayin mai akawu a sashin ajiyar kudi na NNPC.

Mamban kungiyar kwararru

A lokacin rayuwarsa, Egbunike yana daya daga cikin mambobin kungiyar kwararru: kungiyar tsakanin kasa-da kasa na manyan yan sanda (IACP); Kungiyar akawu na Najeriya (ANAN); Kungiyar baristocin Najeriya (NBA); ma'akatar kula da farashi (ICM); Ma'akatar tsare-tsare ta Najeriya (NIM); da kungiyar lura da damfara.

Ya rasu ya bar mata da 'yaya.

Jami’in ‘Dan Sandan da ya yi bincike kan Abba Kyari ya mutu kwatsam a ofis

A wani labari na daban, Joseph Egbunike, wanda shi ne Mataimakin Sufeta-Janar mai kula da sashen FCID na rundunar ‘yan sandan Najeriya ya kwanta dama.

Kara karanta wannan

Auran Sarauta: Sarkin Iwo zai angwance da jikar Sarkin Kano Ado Bayero, Firdausi

Rahoton da ya fito daga Punch a ranar Laraba, 9 ga watan Maris 2022 ya tabbatar da wannan labari.

Kamar yadda mu ka ji, DIG Joseph Egbunike ya fadi ne cikin ofishinsa a yammacin ranar Talata. Tun daga nan bai farfado ba, sai dai aka dauki gawarsa.

Kafin rasuwarsa, Egbunike shi ne 'dan sandan da ya jagoranci kwamitin da IGP Usman Alkali Baba ya kafa domin ya binciki abokin aikinsa, Abba Kyari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng