Jami'an DSS Sun Harbe Wani Soja Har Lahira a Jihar Legas

Jami'an DSS Sun Harbe Wani Soja Har Lahira a Jihar Legas

  • Ana zargin wasu jami’an rundunar tsaro ta fararen kaya, DSS da harbin wani soja, Private Obafemi Adetayo, wanda bayan nan ya mutu a wuraren Lekki da ke Jihar Legas
  • An tattaro bayanai akan yadda jami’an suka harbi Adetayo a cikin sa a makwanni uku da suka gabata yayin da ya yi kokarin fitar da katin shaidar sa
  • Tun bayan harbin ya fadi rai a hannun Allah, a ranar Litinin ya rasa ran sa kamar yadda wata ‘yar uwarsa ta shaida a shafin ta na Twitter cike da takaici da radadi

Legas - Ana zargin wasu jami’an DSS da har yanzu ba a gano sunayen su ba da harbin Private Obafemi Adetayo, wani soja inda ya rasa ran sa a wuraren Lekki da ke Jihar Legas, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Ministan Buhari Ya Ce Yana Shawara Domin Fitowa Takarar Kujerar Shugaban Kasa

An tattaro yadda suka harbe shi a cikin sa a makwanni 3 da suka gabata yana tsaka da dauko katin shaidar sa daga aljihun sa.

Jami'an DSS Sun Harbe Wani Soja Har Lahira a Jihar Legas
Jami'an DSS Sun Bindige Wani Soja Har Lahira a Legas. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Bayan harbin ya fadi ranga-ranga ba tare da sanin inda yake ba, sannan daga bisani ya rasa ran sa a ranar Litinin.

‘Yar uwar mamacin ta bayyana yadda lamarin ya faru a shafin ta na Twitter, inda ta ce duk yadda likitoci suka yi kokarin ceto rayuwarsa sun kasa.

Silar mutuwar jami'in sojan

Kamar yadda ta wallafa:

“Yau na rasa dan uwa na. Soja ne shi kafin ya rasu. A’a, Boko Haram basu halaka shi ba, sannan ‘yan bindiga ma basu kashe shi ba. Bai kuma mutu a filin daga ba. Jami’an DSS ne suka halaka shi a Lekki bayan sun harbe shi a ciki yayin da yake kokarin ciro katin shaidarsa.

Kara karanta wannan

Minista ya yi wa daliban jami’a albishir, ASUU ta kusa janye yajin-aikin da ta shiga

“A wannan karon ma, Najeriya ta gaza. Allah sarki! Yana tsaka da rayuwarsa. Mutumin kirki. Kullum cikin murmushi yake. Na kasa yarda da cewa ba zan sake ganin shi ba.
“Rayuwa a Najeriya daidai take da yawo cikin bama-baman da aka shirya don su fashe. Ya yi kokarin kare kansa inda yayi kokarin ciro katin shaidar sa daga nan suka harbe shi.”

Kakakin rundunar soji ya tabbatar da aukuwar lamarin

The Punch ta bayyana yadda rundunar sojin Najeriya ta 81, Manjo Olaniyi Osoba ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace yanzu haka suna ci gaba da bincike don gano wadanda suka yi mummunan aikin.

Kamar yadda ya ce:

“An harbi daya daga cikin sojojin mu a wuraren Lekki kusan makwanni 3 da suka gabata. Mun samu labarin hakan wanda aka yi gaggawar wucewa da shi asibiti yayin da yake cikin mawuyacin hali.
“Sai dai ya rasu yau da safe. Amma muna ci gaba da bincike don gano silar mutuwar tashi.”

Kara karanta wannan

Sanusi II: Abu 1 da ya sa Jonathan da Ganduje suka tsige ni daga CBN da sarautar Kano

Tashin Hankali: Ɗan Sanda Ya Bindige Abokan Aikinsa 6 Har Lahira A Hedkwatar Ƴan Sanda a Maiduguri

A wani labarin, wani jami'in dan sanda mai suna Saja Bello ya bindige tare da kashe a kalla yan sandan sintiri na mobile guda shida a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a rukunin gidaje da ke kwallejin yan sanda na Hedkwatar Yan sanda a Maiduguri a cewar majiyoyi.

Wani babban jami'i ya shaida wa majiyar Legit.ng cewa a halin yanzu ana can an tsare jami'in a sashin binciken manyan laifuka SCID.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164