Yan bindiga sun sake kai mummunan hari jihar Arewa, sun halaka mutane

Yan bindiga sun sake kai mummunan hari jihar Arewa, sun halaka mutane

  • Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kauyen jihar Neja a arewacin Najeriya, sun kashe akalla mutum 5 sun sace wasu
  • Wani mazaunin ƙauyen da ya samu tsira, ya ce maharan sun farmake su da misalin karfe 10:30 na daren ranar Litinin
  • Sakataren gwamnatin Neja, Ibrahim Matane, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace yan JTF sun fatattaki maharan

Niger - Akalla mutum 5 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu yan bindiga suka farmaki ƙauyen Paikpa kusa da Sarkinpawa, ƙaramar hukumar Munya, a jihar Neja.

Jaridar This Day ta rahoto cewa mutanen ƙauyen da dama sun jikkata, kuma maharan sun yi awon gaba da dabbobin al'umma da yawan gaske.

Lamarin ya auku da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Litinin, lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen kan Babura kowanen su ɗauke da bindigar AK-47.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai kazamin hari hanyar Birnin Gwari-Kaduna, sun yi barna mai muni

Yan bindiga
Yan bindiga sun sake kai mummunan hari jihar Arewa, sun halaka mutane Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa yan ta'addan sun shiga kauyen ta yankin Lawi, hakan ya ba mazauna garin damar tserewa ta wasu hanyoyi na daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan, yan bindigan sun hari yankunan Njita da Chibani, inda suka tasa mutane da dama suka saci dabbobin kafin daga bisani su kama hanyar kauyen Paikpa.

Ɗaya daga cikin mutanen kauyen da suka tsira daga harin, ya bayyana cewa:

"Yan bindigan sun shafe awanni suna aikata ɗanyen aikin su, suka tarwatsa gidajen mutane ba tare da jami'an tsaron da aka jibge a Sarkinpawa sun kawo ɗauki ba."

Ya ƙara da cewa bayan kammala ta'addancin su, yan bindigan sun tsere zuwa cikin dajin Chikun, a jihar Kaduna.

Shin hukumomin sun samu rahoto?

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar da lamarin, amma ya ce har yanzun ba su samu alƙaluman mutanen da harin ya shafa ba.

Kara karanta wannan

Mazauna sun tsere daga kauyukan Filato yayin da yan bindiga ke tsananta kai hare-hare

Matane ya ce yan bindiga sun shiga ƙauyen Paikpa da daren ranar Litinin, kuma suka sace mutane da kuma dabbobi.

A kalamansa ya ce:

"Jami'an kungiyar JTF da kuma Yan Bijilanti sun gwabza da maharan na tsawon awanni, kuma hakan ya sa yan bindigan tsere wa daga harin."

A wani labarin na daban kuma Shugaban EFCC ya goyi bayan kalaman Obasanjo kan masu neman gaje Buhari a 2023

Shugaban hukumar EFCC ya ce maganar Obasanjo gaskiya ce, amma hukumarsa ba ta da hurumi har sai alkali ya yanke hukunci.

Obasanjo ya yi ikirarin cewa da EFCC na aikinta yadda ya kamata da duk masu son gaje Buhari na ɗaure a gidan Yari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262