Na Gwammace In Biya N415,000 in Tafi Ukraine In Zama Bawa, Ɗan Najeriya Ya Yi Ɓaɓatu A Bidiyo

Na Gwammace In Biya N415,000 in Tafi Ukraine In Zama Bawa, Ɗan Najeriya Ya Yi Ɓaɓatu A Bidiyo

  • Wani dan Najeriya ya ce ya gwammaci ya tafi Ukraine a matsayin bawa akan ya tsaya a kasar sa ta gado, wato Najeriya
  • Mazaunin Abujan ya bayyana wa Legit TV ra’ayin nan nasa yayin da ake tambayarsa idan zai iya biyan $1,000 don tafiya Ukraine
  • Mutumin ya kara da cewa gara ya mutu a Ukraine akan ya tsaya yana fama da wahalhalun da ke Najeriya ya kuma mutu a banza

Abuja - Wani mazaunin garin Abuja ya koka akan mawuyacin halin da Najeriya take ciki inda yace ya gwammaci ya biya $1,000 wato N415,000 a matsayin kudin jirgi don ya shiga cikin sojojin Ukraine maimakon ya tsaya a Najeriya.

Ofishin jakadancin Ukraine ta sakataren su na biyu, Bohdan Solty a ranar Alhamis, 3 ga watan Maris ta bayyana yadda suka shirya tsaf wurin kwashe duk wasu ‘yan Najeriya da ke shirin tafiya kasar amma da sharadin kawo $1,000 don kudin jirgi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jirgin jigilar yan Najeriya mazauna Ukraine na biyu ya dira birnin tarayya Abuja

Na Gwammace In Biya $1,000 in Tafi Ukraine In Zama Bawa, Ɗan Najeriya Ya Yi Ɓaɓatu A Bidiyo
Na Gwammace In Biya $1,000 in Tafi Ukraine In Zama Bawa, Ɗan Najeriya Ya Fadi a Bidiyo. Hoto: Legit.ng
Asali: Facebook

Yayin tattaunawa da Legit TV inda aka yi masa tambayoyi, mutumin ya caccaki Buhari akan ba kasar Afghanistan $1m yayin da kungiyar malaman jami’a, ASUU take tsaka da yajin aiki.

Ya kuma soki shugaba Buhari akan tafiya Turai don a duba lafiyar sa.

Ya ce ya gwammaci zama bawa a Ukraine

Mutumin ya kara da cewa babu wani abu mai kyau da ke Najeriya inda yace gara ya yi tafiyarsa Ukraine ya dinga bauta akan ya zauna a Najeriya.

A cewarsa, zai iya daukar matarsa don su wuce Ukraine duk da tashin hankali da rikicin da ake yi. Kamar yadda ya shaida cikin fushi:

“Zan iya daukar mata ta da ke da ciki har zuwa Ukraine don in yi aiki mu mutu a can. Na gwammaci hakan akan ta mutu a asibitin Najeriya wanda babu kayan aiki da gadaje."

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

Amma akwai ‘yan Najeriyan da basu amince da wannan ra’ayin nasa ba

Kelvin Maldini ya ce:

“Duk wanda zai iya biyan $1,000 don zuwa yaki wata kasa wacce ba lallai ya dawo da ran sa ba, babban wawa ne. Da kanka ka dinga yi wa kanka fatan mutuwa.”

Anthony Onifade O ya rubuta:

“Da alamu akwai wadanda basu san ma’anar bauta ba. Idan ka fuskanci bakar azaba daga shugaban ka, zaka gane buredi fulawa ne.”

Abraham Rain ya ce:

“Wancan mutumin so yake yi ya kwashe iyalinsa zuwa Ukraine? Meyasa? Saboda su guje wa talauci!. Ba laifin sa bane, mutanen kasar nan suna cikin tashin hankali, shugabannin kasar nan suna da matsala.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164