Tashin Hankali: Yan bindiga sun bindige Yan Sa'kai sama da 60 a jihar Kebbi
- Wani lamari mara daɗi da ya auku a jihar Kebbi, ya yi sanadin mutuwar jami'an Bijilanti sama da 60 a rana ɗaya
- Tawagar jami'an Bijilanti waɗan da ake kira yan Sa'akai sun tsinci kan su a tarkon yan bindiga lokacin da suka yi kokarin kai musu farmaki
- Hukumomin ba su ce komai ba game da lamarin, kuma tuni aka gudanar da jana'izar waɗan da abin ya auku da su
Kebbi - Yan Bijilanti, waɗan da aka fi sani da yan Sa'kai aƙalla mutum 63 suka rasa rayuwarsu a hannun yan bindiga a jihar Kebbi.
Daily Trust ta rahoto cewa, mummunan lamarin ya auku ne bayan jami'an Sa'kai sun kaddamar da yaƙi da yan ta'addan a yankin masarautar Zuru a jihar Kebbi.
A halin yanzun an gudanar da jana'izar waɗan da lamarin ya faɗa kan su, kuma lamarin ya auku ne da tsakar daren ranar Litinin.
Yadda mummunan lamarin ya auku
Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun ɗana wa Yan Sa'akai tarko, inda suka buya a jikin bishiyoyi a kan hanyar da zata kai zuwa maɓoyar su.
Yan bindigan suka bude musu wuta bayan sun faɗa tarkon su, ba zato ba tsammani Yan Bijilanti suka tsinci kan su a tsakiyar abin harin su.
Jami'an Yan Sa'kai din waɗan da lamarin ya auku da su, sun fito ne daga garuruwa daban-daban da kuma yan Bijilantin Masarauta.
Har zuwa yanzun da muka haɗa wannan rahoton hukumomin tsaro da gwamnati ba su ce komai ba game da mummunan lamarin mara daɗin ji.
A wani labarin kuma Zulum ya ce Insha Allah zamu maida Magidanta 500 gidajen su, mu ba kowa N100,000 ya ja jali kafin Ramadan
Gwamna Zulum na Borno ya ce gwamnatinsa zata yi kokarin maida magidanta 500 daga Malam-Fatori gidajen su kafin watan Ramadan.
Zulum ya ce Insha Allahu gwanatinsa zata maida su gida tare da tallafin N100,000 ga kowane mutum ɗaya.
Asali: Legit.ng