Don Allah kada ku kai mu magarkama: Abba Kyari da 'yan tawagarsa sun roki kotu
- A yau ne aka gurfanar da Abba Kyari da wasu mutanen da ake zargi da harkallar miyagun kwayoyi a kotun Abuja
- Bayan sauraran bayanai daga bangarorin masu kara da wadanda ake kara, Kyari ya nemi kada a kai shi gidan yari
- Ya bayyana haka ne tare da sauran wadanda ake tuhumar, kuma kotu ta amince da bukatar Abba Kyari
FCT, Abuja - DCP Abba Kyari, wanda ke fuskantar tuhumar safarar miyagun kwayoyi a ranar Litinin a gaban kotu, ya roki babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja da kada ta tsare shi a gidan yari.
Kyari, ta bakin lauyansa, Mista Kanu Agabi, SAN, ya roki kotun da ta ba shi damar ci gaba da kasancewa a hannun hukumar NDLEA, har zuwa lokacin da za a saurare shi tare da tantance bukatar neman belinsa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kyari, wanda a baya yake jagorantar rundunar IRT ta 'yan sanda da aka rushe, ya bukaci hakan ne bayan da ya ki amsa laifuka takwas da NDLEA ta gabatar akansa a gaban kotu.
A bangare guda, an samu wasu mutum biyu daga cikin 'yan tawagar Kyari da suka amsa laifin nasu a gaban kotu.
Caccaka tsinke tsakanin lauyoyinsu Kyari da lauyan NDLEA
Jim kadan bayan haka, NDLEA ta hannun Daraktanta mai kula da harkokin shari’arsa, Mista Joseph Sunday, ta nemi a sanya ranar da za a yi shari’a tare da sake duba hujjoji kan wadanda ake tuhumar da suka amsa laifin da ake tuhumar su da su.
Hakazalika hukumar ta NDLEA ta shaida wa kotun cewa ta shigar da bukatar kafa hujjojin ne domin nuna adawa da sakin Kyari da sauran jami’ai hudun da suka musanta laifinsu da sunan beli.
Sai dai, Agabi, SAN, ya yi jayayya cewa tuhumar da ake yi wa su Kyari na kunshe da laifukan da za a iya bayar da belinsu, ya bukaci kotun da kada ta amince da bukatar neman hujjoji game da Umeibe da Ezenwanne.
Ya kuma yi tsokaci kan cewa, wadanda ake tuhumar bisa rashin sani suka amsa laifukan da ake tuhumarsu da su.
Bayan ya saurari bahasi daga bangarorin biyu, mai shari’a Nwite da ke shari’ar ya ce zai bukaci bangarorin su yi magana a hukumance a kan batun a ranar Litinin mai zuwa.
Kotu ta ki ba da belin Kyari, kana ta dage ci gaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar Litinin, 14 ga watan Maris, kamar yadda Punch ta ruwaito.
DCP Abba Kyari da mutum 6 sun bayyana a kotu, za a gurfanar da su
A tun farko, Abba Kyari da wasu mutane shida da ake zargi da hannu wajen badakalar miyagun kwayoyi sun bayyana a harabar babban kotun tarayya a Abuja.
The Nation ta kawo rahoto a safiyar Litinin, 7 ga watan Maris 2022 cewa DCP Abba Kyari sun shigo kotu, ana sauraron a gurfanar da su a gaban Alkali.
Jami’an hukumar NDLEA mai yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ne suka kai Kyari da ragowar ‘yan sanda da mutane biyu da ake zargi zuwa kotu.
Asali: Legit.ng