Karar kwana: Kasa ta rufta da mutum 5 a garin taya abokinsu hakar kasar ginin aurensa

Karar kwana: Kasa ta rufta da mutum 5 a garin taya abokinsu hakar kasar ginin aurensa

  • Rundunar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana yadda wasu mutane biyar suka mutu yayin hakar yashi
  • Rahoto daga majiyoyi ya bayyana cewa, mutanen suna aikin taya abokinsu hakar yashin ginin aurensa
  • An mika gawarwakin matattun ga rundunar 'yan sanda kana ga hakimin kauyen Yanlami da ke Bichi a Kano

Bichi, Kano - Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane biyar da suka makale a karkashin tulin yashi a kauyen Yanlami da ke karamar hukumar Bichi.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara Saminu Abdullahi ya raba wa manema labarai ranar Lahadi a Kano, ta ce lamarin ya faru ne da safiyar Asabar.

Rasuwar wasu mutane a jihar Kano
Mutane biyar sun mutu a yayin da suke hako yashi a Kano | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Abdullahi ya fadi a wani yankin sanarwar da Legit.ng Hausa ta tattaro daga jaridar Premium Times cewa:

Kara karanta wannan

Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri

“Mun samu kira daga ofishin kashe gobara na Bichi cewa ramin ya rufta da mutane biyar. Mun aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:05 na safe."

Ya bayyana sunayen wadanda abin ya rutsa dasu da Alasan Abdulhamid mai shekaru 22 da Jafaru Abdulwahabu mai shekaru 30 da Jibrin Musa mai shekaru 30 da Masaudu Nasiru mai shekaru 25 da kuma Muhammad Sulaiman mai shekaru 35.

Hakazalika, jaridar The Guardian ta ruwaito wani yankin sanarwar na cewa:

“Wadanda abin ya rutsa da su sun makale ne a lokacin da suke aiki a wani kududdufi domin su hakar yashi da nufin su taimaka wa abokinsu da ke ginin aure. Wani bangare na yashin ya rufta ya rufe su kuma suka mutu daga baya."

Kara karanta wannan

Wuta ta lakume kayayyakin sama da miliyan N18m a siton SEMA a jihar Kano

Ya ce an mika gawarwakin matattun zuwa ga rundunar ‘yan sanda da hakimin kauyen Yanlami.

Wata Wuta ta lakume kayayyakin sama da miliyan N18m a siton NEMA a jihar Kano

A wani labarin, wata wuta da ta tashi ranar Jumu'a da yamma a siton hukumar kai agajin gaggaywa SEMA ta lakume kayayyakin da suka kai darajar miliyan N18.5m.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wutar ta yi wannan aika-aika ne a Siton SEMA dake Mariri, ƙaramar hukumar Kumbitso, jihar Kano.

Sakataren hukumar SEMA, Dakta Saleh Jili, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin hira da manema labarai a Kano ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.