Mutane sun yi mamakin yadda na zama dan bindiga, ni makiyayi ne: Bello Turji

Mutane sun yi mamakin yadda na zama dan bindiga, ni makiyayi ne: Bello Turji

  • Bello Turji ya bayyana cewa asalin makiyayi ne wanda ke sayar da Shanu a kasuwa ranar kasuwa
  • Turji, wanda kasurgumin dan bindiga ne mai garkuwa da mutane ya yi sanadiyar asarar rayukan mutane da dama
  • A hirar da yayi da yan jarida, yace mutane na matukar mamakin yadda yya zama dan ta'addan daji

Zamfara - Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya bayyana cewa asalinsa makiyayi ne kuma mutane suna mamakin yadda ya zama dan ta'adda mai garkuwa da mutane.

Bello Turji na daya daga cikin yan bindigan da suka addabi Arewacin Najeriya.

Turji, wanda dan asalin garin Fakai a karamar Shinkafi na jihar Zamfara ne, ya bayyana cewa wadanda suka san shi sun yi mamakin yadda ya fara sata da kashe-kashe.

Kara karanta wannan

Katsina: Yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota, sun kashe fasinjoji 5

A hirar da yayi da tashar Trust TV, Turji yace:

"A baya ni makiyayi ne. Idan mahaifi na na son sayar da Shanunsa, ni ke kai masa kasuwa. Idan na sayar sai in tafi fadar Sarkin Shinkafi kafin in koma gida."
"Sarkin Shinkafi ya san ni. Idan aka fada masa Turji zai zama dan bindiga, ba zai yarda ba saboda ya san mu Fulani ba zamu zama barayin Shanu ba. Amma abubuwan da ake mana ya fara yawa."

Bello Turji
Mutane sun yi mamakin yadda na zama dan bindiga, ni makiyayi ne: Bello Turji Hoto: TrustTV
Asali: Facebook

Turji ya kara da cewa a rana guda aka kashe masa yan uwa shida bayan sacewa iyayensa Shanu sama da dubu.

A cewarsa, sun je dukka kotunan duniyan nan amma Shanunsu basu dawo ba

"An kwashe mana sama da Shanu 1000. A ranar, an kashe yan uwana shida. Iyayenmu sun je kotu amma a dawo musu da Shanunsu ba. Hakazalika an hada kai da yan sa kai wajen kashe babban yayana. Ina talaka zai samu adalci.?"

Kara karanta wannan

Babu ruwanmu da yan Boko Haram, bamu da wata Akida: Bello Turji

Babu ruwanmu da yan Boko Haram, bamu da wata Akida: Bello Turji

Barandanci, ta'addanci, garkuwa da mutane sun zama ruwan dare a Arewacin Najeriya musamman yankin Arewa maso yamma.

Jihohin dake fama da matsalar yan bindiga sun hada da Zamfara, Katsina, Sokoto, Kaduna, da Neja.

A jihar Zamfara kadai, an raba mutane akalla 785,000 da muhallansu.

Tashar Trust TV ta zanta da kasurgumin jagoran yan bindiga Bello Turji, inda ya bayyana cewa ba shi da alaka da yan Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng