Da duminsa: Jirgin jigilar yan Najeriya mazauna Ukraine na uku ya dira birnin tarayya Abuja

Da duminsa: Jirgin jigilar yan Najeriya mazauna Ukraine na uku ya dira birnin tarayya Abuja

  • Gwamnatin tarayya na cigaba da jigilar yan Najeriya da yaki ya rutsa dasu a kasar Ukraniya
  • Tun lokacin da yakin ya barke, wasu sun gudu Romania, Hungary, Slovakia da Poland don neman mafaka
  • Yau kwana goma kenan ana cigaba da gwabza yaki tsakanin kasar Rasha da Ukraine

FCT Abuja - Jirgin jigilar dalibai da yan Najeriya mazauna kasar Ukraine na uku ya bira birnin tarayya Abuja da daren Juma’a, 4 ga watan Maris, 2022.

Jirgin Air Peace dauke da yan Najeriyan ya dira tashar Nnamdi Azikiwe misalin karfe 11 na dare, rahoton TheNation.

Wannan shine kashi na uku na yan Najeriya da aka kwaso daga Ukraine.

Kara karanta wannan

Ukraine: Hotunan 'Yan Najeriya 121 Da Suka Iso Daga Poland Cikinsu Har Da Jinjiri

Da daren jiya, Jirgin jigilar dalibai da yan Najeriya mazauna kasar Ukraine na biyu ya bira birnin tarayya Abuja da yammacin Juma'a

Hazalika da safe jiya da safe mun kawo muku cewa yan Najeriya da aka kwaso a yayin da ake tsaka da yakin Rasha da Ukraine sun iso babbar birnin tarayya, Abuja.

Sun isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 7:11 na safiyar yau Juma’a, 4 ga watan Maris, a jirgin Max Air.

Jaridar The Nation ta kuma rahoto cewa gwamnatin tarayya za ta baiwa kowannen su dala 100.

Yakin Rasha da Ukraniya zai tada Farashin kayan abinci a Najeriya, Asusun lamunin duniya IMF

Asusun lamunin duniya IMF ya bayyana cewa Najeriya da sauran kasashen Afrika na cikin halin barazanar tashin farashin kayan abinci, da man fetur sakamakon yakin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine.

Dirakta Manaja na IMF, Ms Kristalina Georgieva, ta bayyana hakan bayan ganawa da Ministocin kudin kasashen Afrika, gwamnonin bankuna kasa, wakilan majalisar dinkin duniya don tattauna illar da yakin Ukraine ka iya wa nahiyar, rahoton US News.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa a yaki

A cewarta, asusun IMF shirya yake da taimakawa kasashen Afrika wajen dakile illolin yakin ta hanyar samar da tsare-tsare na shawari da bashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng