Tashin Hankali: Ɗan Sanda Ya Bindige Abokan Aikinsa 6 Har Lahira A Hedkwatar Ƴan Sanda a Maiduguri
- Wani jami'in dan sanda, Bello, mai mukamin saja, ya bude wa abokan aikansa wuta ya halaka 6 ya kuma raunata biyu a Maiduguri, Jihar Borno
- Rahotanni sun nuna cewa dan sandan ya kuma harbi surukinsa bayan matarsa ta bar gidansa a baya-bayan nan saboda rashin jituwa da suke samu
- Wata majiya ta ce a baya-bayan nan dan sandan ya samu matsala da matarsa har da ta bar gidansa duba da cewa makwabtan sun yi kokarin sulhunta su amma bai yiwu ba
Jihar Borno - Wani jami'in dan sanda mai suna Saja Bello ya bindige tare da kashe a kalla yan sandan sintiri na mobile guda shida a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a rukunin gidaje da ke kwallejin yan sanda na Hedkwatar Yan sanda a Maiduguri a cewar majiyoyi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani babban jami'i ya shaida wa majiyar Legit.ng cewa a halin yanzu ana can an tsare jami'in a sashin binciken manyan laifuka SCID.
Dan sandan ya samu rashin jituwa da matarsa a gida
Wani majiya daga iyalansa ya ce sajan ya samu rashin jituwa da matarsa kuma makwabta sun yi kokarin sulhu amma bai saurare su ba.
"Sun dade suna samun rashin jituwa da matarsa; mun yi kokarin sulhunta su amma bai yarda ba.
"Matar ta fada wa iyayenta cewa sajan ya doke ta; ta bar masa gidansa. Matar ta bar gidan saboda rashin kyautatawa daga mijinta.
"Ya fara harbe-harbe yana barazanar zai kashe kowa. Ya bindige mutune, yan sanda shida sun mutu wasu biyu suna asibiti ana musu magani.
"Ya kona gidaje biyu da dakuna takwas kuma ya harbi surukinsa," in ji majiyar.
Ba a samu ji ta bakin rundunar yan sanda ba game da afkuwar lamarin
Daily Trust ta rahoto cewa an yi kokarin ji ta bakin kakakin yan sandan jihar Borno amma hakan bai yiwu ba domin wayansa na kashe a lokacin hada wannan rahoton.
'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe
A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.
Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.
Asali: Legit.ng