Kamar almara: An haramtawa Magen Rasha shiga kasar wasanni bisa mamayar Ukraine
- Kungiyar Mage ta majalisar dinkin duniya ta haramtawa Maguna daga kasar Rasha shiga gasar wasanni
- Wannan na zuwa ne bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar soji a kasar Ukraine a makon jiya
- Wannan lamari ya tayar da hankalin shugabannin duniya, inda ake ci gaba da Allah wadai da lamarin
Faransa - Kungiyar Mage ta Duniya ta ce ta haramtawa Magunan Rasha shiga gasarta a matsayin ladabtar da Shugaba Vladimir Putin bisa farmakar Ukraine, The Cable ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, kungiyar - wacce ke alfahari da kanta a matsayin "Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya ta Maguna" - ta ce "ta firgita kuma ta jijjiga" da ta ji cewa sojojin Rasha za su mamaye Ukraine tare da "fara yaki."
Kungiyar da ke Faransa - wacce kuma aka sani da Fédération Internationale Féline (FIFe) - ta ce ta yanke shawarar ne a ranar Talata, saboda ba za ta iya ganin wannan ta'asa ba kuma ba ta yi komai ba.
FIFE ta ce haramcin zai ci gaba da kasancewa har zuwa karshen watan Mayu sannan kuma za a sake duba shi.
Ya ake gasar kungiyar Mage?
A cewar shafin yanar gizon FIFé an kafa kungiyar ne a 1949 kuma tana daukar nauyin wasanni 700 a kowace shekara, inda ake baje kolin Maguna sama da 200,000.
Takunkumin ya zo ne a daidai lokacin da Warner Bros., Disney, da kuma Sony suka ba da sanarwar cewa ba za su fitar da fina-finansu na baya-bayan nan a gidajen sinima na Rasha ba.
Gwamnatoci a duk faɗin duniya suna ta kara sanya takunkumi kan Shugaba Putin da kasarsa Rasha.
A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, kamfanoni na duniya, ciki har da masu kera motoci da masu samar da makamashi, sun yanke huldar kasuwanci da Rasha.
Wannan kenan tun bayan da Rasha ta fara aiwatar da mamayar soja a kasar Ukraine a makon jiya.
Zama na biyu na tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine
A wani labarin, a yau ne wakilai daga kasashen Rasha da Ukraine za su gana a zagaye na biyu na tattaunawar sulhu a iyakar kasar Belarus.
Tashar talabijin ta CNN ta ba da rahoton cewa, Mykhailo Podolyak, mashawarci ga shugaban kasar Ukraine ya bayyana cewa wakilansu na kan hanyarsu ta zuwa tattaunawar.
Andrew Simmons na Aljazeera, dake dauko rahoto daga birnin Lviv da ke yammacin kasar Ukraine, ya ce babu wani sa rai da a zagaye na biyu na tattaunawar da za a yi na cimma wata yarjejeniya kan kawo karshen yakin.
Asali: Legit.ng