Birbishin rikici a Filato yayinda aka hallaka Shanu 100 ba gaira ba dalili

Birbishin rikici a Filato yayinda aka hallaka Shanu 100 ba gaira ba dalili

  • Wasu yan bindiga sun dira jihar Plato inda suka hallaka dabbobin makiyaya ba gaira ba dalili
  • Shugabannin kungyaoyin Fulani makiyaya na yankin sun yi Ala-wadai da wannan abu
  • Har yanzu ba'a samu ji daga bakin hukumomin jihar ba

Jos South - Ana fargabar rikici a karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau sakamakon kisa da jikkata Shanu sama da 100 da wasu yan bindiga sukayi ranar Laraba, 2 ga Maris, 2022.

Daily Trust ta ruwaito Shugaban kungiyar makiyayan Gan Allah (GAFDAN), Abdullahi Shehu, da cewa wannan abu ya faru ne da yamma lokacin da Shanun ke kiwo.

Birbishin rikici a Filato yayinda aka hallaka Shanu 100 ba gaira ba dalili
Birbishin rikici a Filato yayinda aka hallaka Shanu 100 ba gaira ba dalili
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, bayan Shanun da aka hallaka, an nemi Raguna da Tinkiyoyi da dama an rasa.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun bayyana gaskiyar abin da yasa Fulani Makiyaya suka halaka mutum 7 a Taraba

Shehu yace:

"Shanun na kiwo ne lokaci da yan bindigan suka dira unguwar Maiyanga suka fara harbi. Kawo yanzu dai an kashe shanu 100 yayinda ba'a ga wasu ba."
"Mun sanar da yan sanda da rundunar Operation Safe Haven. Kwamandan Sector 3 ya amsa kiranmu kuma an damke mutum bakwai dake da alaka da kisan."
"Mun gaji da wannan abu. Laifin me mukayi? Bamu lalata gonan kowa ba. Muna kira ga jami'an tsaro suyi abinda ya dace don gano wadanda sukayi wannan aika-aikan."

Shugaban kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) na jihar, Mallam Nura Abdullahi, hakazalika ya tabbatar da labarin.

Har yanzu dai hukumar yan sandan jihar bata yi tsokaci kan lamarin ba.

Gwamnan Abia zai biya diyyan N2m ga iyalan Hausawan da aka kashe a kasuwar dabbobi

A wani labarin kuwa, mukaddashin shugaban kungiyar dilolin dabbobin Najeriya, Yahuza Yusuf, ya bayyana cewa Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya yi alkawarin biyan kudin diyyan N2m ga iyalan kowani mutum guda cikin wadanda aka kashe a kasuwar dabbobi a jihar.

Kara karanta wannan

Babu ruwanmu da yan Boko Haram, bamu da wata Akida: Bello Turji

Yahuza, ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayinda wakilan gwamnatin jihar Abia karkashin Sarkin masarautar Abiriba, Kalu Ogbu, suka ziyarci gidan gwamnatin jihar Gombe, rahoton Cable.

Mafi akasarin Hausawan da aka kashe a harin yan asalin jihar Gombe ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng