Ku kwantar da hankulanku, muna da litan mai 1.7bn: Shugaban NNPC ga yan Najeriya

Ku kwantar da hankulanku, muna da litan mai 1.7bn: Shugaban NNPC ga yan Najeriya

  • Shugaban kamfanin NNPC ya ce daga yanzu za'a fitar da mai daga Depot babu dare, babu rana don rage wahalar man da ake yi
  • Mele Kyari yace kamfanin na da litan mai kimanin bilyan biyu yanzu a ajiye kuma za'a fara fitarwa
  • Ya baiwa yan Najeriya hakuri bisa halin wahala da tsadar mai da suke fama da shi

Abuja - Kamfanin man Najeriya NNPC ya yi kira ga yan Najeriya su daina tada hankulansu suna ajiyan man fetur saboda akwai isasshen mai a ajiye da za'a fitar.

Dirakta Manaja na NNPC, Mele Kyari, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Abuja ranar Laraba bayan ganawarsa da kungiyar ma'aikatan man fetur da kungiyar direbobin tankan mai (PTD).

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

Sauran kungiyoyin dake hallare a ganawar sun hada da kungiyar yan kasuwar mai na Depot, DAPMAN, da kungiyar manyan yan kasuwan mai MOMAN.

Yace:

"Babu karancin mai a kasar nan. Abinda kuke gani da layukan mai wahala ce kawai. Mutane su sayi daidai abinda suke bukata."
"Muna tabbatar muku da cewa muna da isasshen man fetur da kowa zai samu, amma muna bada hakuri bisa wahalar da mutane ke sha."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban NNPC ga yan Najeriya
Ku kwantar da hankulanku, muna da litan mai 1.7bn: Shugaban NNPC ga yan Najeriya Hoto: NNPC
Asali: UGC

Muna da litan mai litan 1.7bn

A cewarsa, Najeriya na da isasshen man da zata fitar da mai daga Depot don takaita wahalar mai.

Yace:

"Kawo yanzu akwai litan mai bilyan 1.7 hannunmu a kan ruwa da tudu. Hakan na nufin cewa muna da ikon fitar da mai daga Depot dinmu duka."
"Mun shirya yadda za'a fitar da mai a Depot ba dare, ba rana."

Kara karanta wannan

Rashin mai da rashin wuta: Ku cigaba da juriya, ai ba mulkin Buhari aka fara rashin ba: Femi Adesina

"Wannan zai taimaka wajen hana ajiyan man da sayan man da mutum bai bukata, kamar yadda muke gani a gidajen mai yau. Abubuwa zasu dawo daidai."

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng