Mamayar Rasha: Mutane miliyan 1 sun yi gudun hijira a Ukraine cikin mako 1, UNHCR
- Kasar Ukraine ta shaida munanan hare-hare daga kasar Rasha a cikin mako guda, lamarin da ya kai ga 'yan kasar suka fara tserewa
- Akalla mutane miliyan daya ne suka bar kasar Ukraine cikin kasa da mako guda, kamar yadda rahotanni suka bayyana
- Wannan lamari dai yana ci gaba da ci wa shugabannin duniya tuwo a kwarya, hakazalika, Rasha na ci gaba da daukar munanan matakai
Ukraine - Mutane sama da miliyan daya ne suka tsere daga Ukraine a cikin mako guda tun bayan da Rasha ta mamaye kasar, inji Majalisar Dinkin Duniya a yau Alhamis.
Hakazalika, majalisar ta yi gargadin cewa matukar dai ba a kawo karshen yakin nan take ba, to akwai yuwuwar wasu miliyoyin za su tsere, kamar yadda Channels Tv ta tattaro.
Shugaban 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi a shafinsa na Twitter ya ce:
"A cikin kwanaki bakwai kacal mun shaida yadda mutane miliyan daya ke gudun hijira daga Ukraine zuwa kasashen makwabta."
Grandi ya yi gargadin cewa:
"Sai dai idan ba a kawo karshen rikicin nan take ba, akwai yuwuwar a tilastawa wasu miliyoyi yin hijira daga Ukraine."
A bayanan UNHCR, mutane 1,002,860 yanzu haka sun tsere daga Ukraine tun lokacin da shugaban Rasha Vladimir Putin ya kaddamar da cikakken mamaya a Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu.
Grandi ya ce yawan 'yan gudun hijiran karuwa yake cikin sauri mai ban mamaki, inji makalar da UNHCR ta wallafa a shafinta na yanar gizo.
Ya kuma bayyana cewa, a tsawon shekaru sama da 40 da yake aikin kula da 'yan gudun hijira, bai taba ganin yadda adadi ke yawan karuwa kamar na Ukraine ba.
Fiye da rabin wadanda suka tsere daga Ukraine sun tsallaka zuwa makwabciyarta Poland. Hungary, Moldova da Slovakia suma sun yi maraba da 'yan gudun hijira da dama.
Mun zo taya ku yakar Rasha: Dandazon 'yan Najeriya sun cika ofishin jakadancin Ukraine
A bangare guda, kimanin matasa 115 ‘yan Najeriya ne, a ranar Talata, 1 ga watan Maris, suka nuna sha'awar shiga yakin kasar Ukraine da Rasha.
Matasan da suka yiwa ofishin jakadancin Ukraine da ke Abuja babban birnin Najeriya kawanya, sun kuma sanya sunayensu a cikin wata rajista da ofishin jakadancin ya bayar.
Jaridar Guardian ta rawaito cewa jami'an ofishin jakadancin sun dakile yunkurin daukar hotunan mutane a bakin ofishin.
Asali: Legit.ng