Kafin karshen watan nan zan fita daga jam'iyyar PDP, Rabiu Musa Kwankwaso

Kafin karshen watan nan zan fita daga jam'iyyar PDP, Rabiu Musa Kwankwaso

  • Daga karshe, Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa zai sauya sheka daga jam'iyyar PDP
  • Wannan shine karo na uku da Kwankwaso zai sauya shekar jam'iyya tsakanin shekarar 2014 da yanzu
  • Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta ce suna kan tattaunawa da Sanata Rabiu Kwankwaso akan batun komawar sa jam’iyyar

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa kafin karshen watan nan zai fice daga jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party PDP.

BBC Hausa ta ce tsohon gwamnan ya bayyana mata hakan.

Har ila yau Kwankwaso ya tabbatar da labarin cewa ya yi nisa a shirinsa na komawa jam'iyyar NNPP watau New Nigeria Peoples Party.

Wani makusancin tsohon gwamnan ya ce rashin tsari a game da yadda ake tafiyar da sha'anin jam'iyyar ta PDP ya tilasta wa Sanata Kwankwaso tattara kayansa domin ya fice daga cikinta.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ga Matawalle: Ka daina tursasa mutane don kawai su shiga APC

Rabiu Musa Kwankwaso
Kafin karshen watan nan zan fita daga jam'iyyar PDP, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Senator Rabiu Kwankwaso
Asali: Getty Images

Sauye-sauyen shekar Kwankwaso

A shekarar 2014 Kwankwaso ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

A shekarar 2019, Kwankwaso ya sake komawa PDP daga APC

Yanzu a 2022, Sanatan ya yanke shawarar komawa wata jam'iyya daga PDP

2023: Kwankwaso Zai Dawo Jam’iyyar Mu, NNPP Ta Bayar Da Tabbaci

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta ce suna kan tattaunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso akan batun komawar sa jam’iyyar kafin zuwan zaben 2023, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kamar yadda jam’iyyar ta shaida, nan da ‘yan kwanaki kadan tsohon gwamnan da tawagar sa za su koma jam’iyyar NNPP.

Dama tun a kwanakin baya aka samu bayanai akan yadda Kwankwaso yake shirin komawa wata jam’iyyar don tsayawa takarar shugaban kasa bayan ya soki APC da PDP.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Zai Dawo Jam’iyyar Mu, NNPP Ta Bayar Da Tabbaci

Yayin tattaunawa da manema labarai, shugaban kwamitin zartarwa, NEC na NNPP, kuma sakataren jam’iyyar, Ambasada Agbo Major ya ce sun yi taro ne don tattaunawa akan yadda zasu bunkasa jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng