Zamfara: Yan bindiga sun kaure da fada tsakanin su kan dabbobi, sun yi wa juna barna
- Tawagar yan bindiga biyu ma su hamayya da juna sun kaure da faɗa tsakanin su kan rabon dabbobin sata a jihar Zamfara
- Wani mazaunin kauyen Kunchin Kalgo ya bayyana cewa yan bindiga biyu ne suka rasa rayukansu sanadin faɗa tsakanin su
- Mutane na tsaka da cin kasuwa a kauyen yayin da suka jiyo karar harbi na tashi kowa ya yi ta kansa domin tsira
Zamfara - Musayar wuta ya barke ranar Litinin tsakanin tawagar yan bindiga dake hamayya da juna a kusa da ƙauyen Kunchin Kalgo, karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin, Sani Usman, ya shaida wa Daily Trust cewa yan bindigan sun gwabza tsakaninsu ne kan sabanin da ya shiga game da rabon shanun da suka sato.
Usman ya ce:
"Ranar kasuwa ne a Kunchin Kalgo, mutane sun fara harkokin su na cin kasuwa, yayin da aka fara jin ƙarar harbe-harbe na tashi ba zato ba tsammani."
"Hankulan kowa ya tashi, yan kasuwa suka fara tseren neman tsira da rayuwarsu. Wani mai siyar da waya ne harsashi ya same shi, kuma aka kai shi Asibiti daga baya.
"A halin yanzun biyu daga cikin yan bindigan sun rasa ransu a faɗan. Kasuwar ta koma kamar an yi ruwa an ɗauke babu kowa cikin kankanin lokaci.
Yadda yan ta'adda suka matsa wa yankin
A kwanakin baya, mutane sun ga wasu tawagar yan bindiga ɗauke da makamai a kan babura a ƙauyen Kunchin Kalgo.
Rahoto ya nuna cewa da yuwuwar yan ta'addan sun bata hanyar zuwa inda suka nufa ne domin sun koma cikin jejin Munhaye jin kaɗan bayan zuwan su.
A baya-bayan nan, garin Tsafe da wasu kauyukan dake karkashin karamar hukumar sun sha fama da harin ta'addanci, satar mutane domin neman fansa.
A yanzun da muke haɗa wannan rahoton ba mu sami kakakin rundunar yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ba bare mu ji ta bakin hukumarsu.
A wani labarin kuma Dakarun Rasha sun zagaye birnin da Daliban Najeriya ke ciki a Ukraine, kuma babu wata hanyar fita
Akalla daliban Najeriya 370 dake karatu a ƙasar Ukraine suka makale a birnin Sumy yayin da Dakarun Rasha suka zagaye birnin.
Sakataren Ofishin jakadancin Ukraniya a Najeriya yace ya kamata FG ta tashi tsaye matukar tana son ceton ɗaliban.
Asali: Legit.ng