Ka ba da mu: Rundunar ‘yan sanda ta nemi jami’in da aka ga yana dakon tiren abinci a wurin biki

Ka ba da mu: Rundunar ‘yan sanda ta nemi jami’in da aka ga yana dakon tiren abinci a wurin biki

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce tana bincika wani faifan bidiyo da ke nuna wani jami’inta dauke da tiren abinci ga wata mata da yake kula da ita
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan Muyiwa Adejobi, ya ce an gayyaci jami’in zuwa Abuja, yana mai cewa abin da ya yi abin kunya ne ga martabar rundunar
  • Rundunar ‘yan sandan ta kuma gargadi jami’an da ke aiki da fitattun mutane a duk fadin kasar da su daina gudanar da wasu ayyuka baya ga aikinsu na tsaro

FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gayyaci wani jami'in dan sanda da aka gani kwanan nan a wani faifan bidiyo dauke da tiren abinci na wata fitacciyar mata a wani taron da aka gudanar a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Muyiwa Adejobi, mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar, ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 2 ga watan Maris, inji rahoton The Punch.

Ka ba da mu: Rundunar ‘yan sandan ta nemi jami’in da aka ga yana dakon tiren abinci a wurin biki
Ka ba da mu: Rundunar ‘yan sandan ta nemi jami’in da aka ga yana dakon tiren abinci a wurin biki | Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Ya ce hukumar ‘yan sanda na binciken faifan bidiyon da ke nuna dan sandan dauke da tiren abinci a bayan wata fitacciyar mata a wurin biki.

Legit.ng ta tattaro cewa rundunar ‘yan sandan ta gargadi jami’anta da ke da alaka ko aiki da fitattun mutane a duk fadin kasar nan da su daina yi musu hidimar ta zarce ba da kariya daga barazanar tsaro.

Adejobi ya bayyana cewa:

“An gano shi (dan sandan). Zai zo Abuja ya same mu. Za mu yi masa tambaya kuma mu dauki matakin da ya dace.
"Ya kamata mu hana irin wannan abu saboda abin kunya ne ga martabar Rundunar kuma ba za mu iya ci gaba da ganin irin wannan abu ba saboda rashin kwarewa ne."

Kara karanta wannan

Sojin hadin gwiwa sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a iyakar Kamaru da Najeriya

A cikin faifan bidiyon wanda ya yadu a shafukan sada zumunta, an ga dan sandan da ke tafe a bayan matar dauke da tire cike da abinci yayin da ta yi gaisawa da wata mata a bainar jama'a.

Idan kuka duba da kyau, za ku ga sunan dan sandan a jikin rigars. Sunansa Yahaya Abubakar.

Kalli bidiyon:

'Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu

AWISTO, @Awistot, ya yi sharhi a shafin Twitter:

“Abin da NPF suka mayar da kansu ke nan, sun zaman kamar masu gadin da kawai za ku samu don tsaron gida.
"Ba su da sauran wata kima, kimar da suke da ita ita ce bindigar da suke dauke da ita wacce ita ma din ba wata daraja take basu ba."

Sam Chukwuemeka, @SamChukwuemeka1, ya ce:

"Ban ji dadin kallon wannan faifan ba, idan da gaske dan sandan nan ya dauka mata abinci, gaskiya ta ci mutuncin NPF..."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta ankarar da al’umma, ta ce ayi hattara da boyayyen shirin ‘Yan ta’adda

Black Barbie, @BlackBarbyy, ya ce:

"Daukar tire da jakar kudi ga VIP. Wannan hakika matukar abin kunya ne."

Stanbelo, @chinonsoAwo, ya ce:

"Akwai bukatar mu yi wani abu, 'yan sanda su yi wani abu don kare jami'an 'yan sandanmu, muna bukatar mu gaya wa wadannan mutanen cewa dan sanda ba yaron gida ko mai aiki ba ne abin banza."

Jedidah Bright, @JedidahBright, ya ce:

"Hakan yana faruwa a cikin cibiyoyin gwamnati da dama, rigar ce kawai ta sa wannan cin zarafi ya zama sananne."

Sai dai, a bangare guda Legit.ng ta kuma lura cewa, wasu na da ra'ayin cewa dan sandan na dauke da tiren abincin ne wa karan kansa ba wai na wani bane.

Jakadan Canada a Najeriya ya ziyarci marasa gata a kasan gada, hotunansu suna wasa sun taba zukata

A wani labarin, wanda ya shirya wasan buyan da yaran talakawa ke yi, Tunde Onakoya, ya bada labarin yadda babban kwamishinan Canada, Kelvin Tokar da sauran ma'aikatan suka ziyarci yaran a karkashin gadar Oshodi.

Kara karanta wannan

Bam ya tashi cikin dare a Kaduna – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan abin da ya auku

Hakan ya janyo tsokaci iri-iri a Twitter, a lokacin da ya wallafa bidiyon jakadan da sauran daga HMCS Goose Bay - jirgin ruwan rangadi na Kinston. Kananun yaran sun shiga cikin tsananin farin cikin wasa da turawa.

Babban kwamishinan ya gabatar da kanshi ga dukkan kananun yaran da 'yan anguwan. Haka zalika, mutumin yayi magana a kan alakar Najeriya da Kanada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.