Jakadan Canada a Najeriya ya ziyarci marasa gata a kasan gada, hotunansu suna wasa sun taba zukata
- Jakadan kasar Canada a Najeriya, Kevin Tokar da sauran baki daga kasar waje, duk sun tafi ganawa da yaran dake rayuwa a karkashin gadar Oshodi
- Yaran sun kebe tare da turawan duk da banbamncin launin fata, inda suka ji dadin yadda suke wasan buya da juna
- 'Yan Najeriya da dama sun yi addu'a ga Tunde Onakoya da bawa yaran marasa galihu da saura babbar dama a rayuwa
Legas - Wanda ya shirya wasan buyan da yaran talakawa ke yi, Tunde Onakoya, ya bada labarin yadda babban kwamishinan Canada, Kelvin Tokar da sauran ma'aikatan suka ziyarci yaran a karkashin gadar Oshodi.
Hakan ya janyo tsokaci iri-iri a Twitter, a lokacin da ya wallafa bidiyon jakadan da sauran daga HMCS Goose Bay - jirgin ruwan rangadi na Kinston. Kananun yaran sun shiga cikin tsananin farin cikin wasa da turawa.
Babban kwamishinan ya gabatar da kanshi ga dukkan kananun yaran da 'yan anguwan. Haka zalika, mutumin yayi magana a kan alakar Najeriya da Kanada.
Yaran da aka koyawa wasan buyan sun bayyana a riguna da gajerun wanduna. Dukkan mu maza ne, a cewar Tunde. Yaran sun hadu wurin jakadan da sauran ma'aikatan da suka halarci wurin.
"A wannan lokacin, bamu damu da launin fata, matsayi, tushe ko kasar da mutum yake ba. Mutuntaka ta fi komai. Mu daina amincewa da cewa bambamcin mu ke daukaka ko kaskanta wani daga cikin mu. Dukkan mu mutane ne."
Martanin jama'a
Ga wasu daga cikin tsokacin:
@Janniebabe3 ta ce: "Yayin da kuke cigaba da gina rayuwar yaran nan, kyawawan abubuwa da jin kai ba zai taba kaura daga gareku na tsawon rayuwarku ba. Ina kaunar soyayyar da kuke wa yaran."
@lolitagift cewa tayi: "@Tunde_OD ka yi kokari, ka cigaba da kyakyawan aikin."
@OkoyeJanefranc2 ya ce: "Hakan yayi kyau Tunde, Ubangiji ya cigaba da maka albarka."
@20twoz ya ce: "Na zubda hawayen farin ciki daga idanuwa na. Hakan na da ban sha'awa."
@latmos997 ya ce: "Kai. Hakan yayi kyau, samun zuwa karkashin gadar Oshodi, ai dama ce."
Budurwa ta gwangwaje matashi dake doguwar tafiya zuwa makaranta da dalleliyar mota
A wani labari na daban, jajircewa da neman na kan wani yaro, ya janyo masa kyauta daga wacce bai sani ba da tayi sanadiyyar canza rayuwarshi gaba daya.
Wani yaro dalibin makarantar sakandare dan shekara 18, mai suna Jayden Sutton daga yankin Cobb na Georgia dake Turai, ya sha matukar mamaki yayin da wata mata mai matukar kirkin wacce ta rage mishi hanya a motar ta, ta yi masa gagarumar kyauta.
Becauseofthemwecan ta ruwaito yadda Jayden ke aiki a wurin cin abinci bayan tashi daga makaranta don kawai ya tara kudin cika burin sa na siyan mota.
Asali: Legit.ng