Mun shirya: Najeriya za ta fara gina tashar makamashin nukiliya, ta hada kai da Rasha, da wasu kasashe

Mun shirya: Najeriya za ta fara gina tashar makamashin nukiliya, ta hada kai da Rasha, da wasu kasashe

  • Shirin gwamnatin Najeriya na gina tashar samar da makamashin nukiliya domin magance matsalar wutar lantarkin na kara fitowa fili
  • Bankin Duniya a kwanan nan ya bayyana Najeriya a matsayin wacce ke da mafi munin wutar lantarki a duniya, kuma gwamnatin tarayya za ta yi fatan canza wannan mummunan labari
  • Tuni dai aka kulla yarjejeniya da Rasha da Pakistan domin horar da ‘yan Najeriya yadda za su gudanar da aikin samar da wutar lantarki yadda ya kamata

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yanzu haka an bude yunkurin gwamnati na gina tashar makamashin nukiliya mai karfin megawatt 4000.

A cewar rahoton Nairametrics, Dokta Yau Idris, Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Najeriya (NNRA) ne ya bayyana hakan a yayin wani taron koli na makamashi na kasa da kasa na Najeriya (NIES) da ke gudana a Abuja.

Kara karanta wannan

Duk za mu mutu: Yaro ya fashe da kuka, yana tsoron ka da Rasha ta harbo bam Najeriya

Shugaba Buhari zai kawo karshen matsalar wutan lantarki
Mun shirya: Najeriya don gina tashar nukiliya, sanya hannu da Rasha, da sauransu | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Idan har aka yi nasara aka kammala aikin, Idris ya yi ikirarin cewa masana'antar za ta kasance babbar tashar samar da wutar lantarki a kasar.

Idris ya kuma nuna rashin jin dadinsa ga yadda ‘yan Najeriya da dama ke ganin cewa kasar ba za ta iya sarrafa tashar makamashin nukiliya ba.

Jaridar Daily Sun ta rahoto shi yana cewa:

"An samar da wasu dabaru don tabbatar da cewa kowace kasa za ta iya kafa tashar makamashin nukiliya.
"Najeriya na shirin samar da makamashi mai karfin megawatt 4,000 ta hanyar amfani da fasahar nukiliya. Muna kokarin gina tashoshi hudu kuma muna cikin shirin bayar da kwangilar”.

Ya kuma bayyana cewa FG na ta kokarin karkatarwa da inganta makamashin Najeriya tun a 1977, kuma cibiyar da za a yi mai karfin MW 4,000 zata kara karfin samar da wutar lantarki a Najeriya zuwa 13,000MW.

Kara karanta wannan

Sabon jidali: Tallafin mai zai karu kan FG yayin da farashin mai ya tashi zuwa $112.7 kan kowacce ganga

Idris ya kuma yi ikirarin cewa an cimma yarjejeniya da kasashen Rasha, Pakistan, Faransa, da kuma Koriya ta Kudu domin kara karfin horo ga jami'an Najeriya wajen sarrafa makamashin nukiliya.

Mun zo taya ku yakar Rasha: Dandazon 'yan Najeriya sun cika ofishin jakadancin Ukraine

A wani labarin, kimanin matasa 115 ‘yan Najeriya ne, a ranar Talata, 1 ga watan Maris, suka nuna sha'awar shiga yakin kasar Ukraine da Rasha.

Matasan da suka yiwa ofishin jakadancin Ukraine da ke Abuja babban birnin Najeriya kawanya, sun kuma sanya sunayensu a cikin wata rajista da ofishin jakadancin ya bayar.

Jaridar Guardian ta rawaito cewa jami'an ofishin jakadancin sun dakile yunkurin daukar hotunan mutane a bakin ofishin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.