Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun halaka dandazon mutane
- Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun aikata mummunar ɓarna a kauyen Amangwu Ohafia dake yankin jihar Abia
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun halaka mutane ma su adaɗi mai yawa, wanda har yanzun ba'a gano yawan su ba
- Hukumomin gwamnatin jihar da hukumar yan sanda ba su ce komai ba, yayin da mutane suka fara gudun kauyen don tsira da ran su
Abia - Tsagerun yan bindiga sun halaka adadin mutane mai yawa a wani kazamin hari da suka kai kauyen Amangwu Ohafia, ƙaramar hukumar Ohafia, jihar Abia.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa maharan sun kone gidajen mutanen ƙauyen da dama, konewa kurmus ya yin harin na ranar Talata da daddare.
Wata majiya ta bayyana cewa mutanen ƙauyen sun fara ƙauracewa gidajen su, yayin da suka nemi mafaka a wasu kauyuka dake makwaftaka da su.
TVC News ta rahoto cewa har yanzun gwamnatin jihar Abia ba ta fitar da sanarwa game da mummunan harin da ya auku ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka nan kuma a ɗaya bangaren, rundunar yan sanda reshen jihar, ba tace uffan ba kan adadin yawan al'ummar da ba su ji ba ba su gani ba aka kashe su.
Wane hali mazauna ƙauyen ke ciki?
Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da cewa da yawan mutanen kauyen sun gudu zuwa wasu kauyukan dake kusa domin tsira da rayuwarsa.
A halin yanzun, ragowar dake zaune a yankin da lamarin ya faru na cikin zaman ɗar-ɗar da tsoro, bisa rashin sanin abin da ka iya zuwa ya dawo nan gaba.
A wani labarin na daban kuma Sojoji sun bindige dan ta'adda dauke da bama-bamai a Borno
Yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun kaddamar da shirin kai farmaki nisan kilomita uku zuwa ƙauyen Ajigin Bulabulin, a jihar Borno.
Sai dai yan ta'addan sun gamu da tirjiya daga sojojin, nan take suka aika da ɗan kunan bakin wake, wanda sojojin suka halaka shi tun kafin ya isar da nufinsa.
Asali: Legit.ng