Kisan gillar Hanifa: An hana 'yan jarida daukar rahoton zaman kotu

Kisan gillar Hanifa: An hana 'yan jarida daukar rahoton zaman kotu

  • A yau Laraba, 2 ga watan Maris ne aka ci gaba da shari’ar Hanifa Abubakar, dalibar da ake zargin shugaban makarantarsu da kashe ta a jihar Kano
  • Sai dai kuma Atoni janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano, Musa Lawan, ya hana 'yan jarida shiga kotun da ake ci gaba da sauraren shari'ar kisan nata
  • Lawan ya ce an yi hakan ne domin ba jami’an hukumar tsaro ta farin kaya damar ba da shaida a gaban kotu

Kano - Atoni janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano, Musa Lawan, ya hana yan jarida daukar rahoton zaman shari’ar Abdulmalik Tanko, malamin da ake zargi da garkuwa da kuma kashe daliba yar shekara 5, Hanifa Abubakar.

Mista Lawan ya ce an yanke wannan hukunci ne domin ba jami’an hukumar tsaro ta farin kaya damar ba da sahida a gaban kotu, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta aike mutumin da aka kama da sunki 39 na wiwi gidan gyaran hali

Kisan gillar Hanifa: An hana 'yan jarida daukar rahoton zaman kotu
Kisan gillar Hanifa: An hana 'yan jarida daukar rahoton zaman kotu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya kuma umurci masu daukar rahoto da su bar harabar kotun har zuwa bayan zaman farko (shaidar tsaro).

Mista Tanko da daya daga cikin wadanda ake zargi, Hashimu Isyaku, sun amsa laifin hada baki wajen aikata laifi amma sun karyata sauran tuhume-tuhume hudu a shari’ar kisan kan.

Sai dai kuma, dayan wacce ake zargi, Fatima Jibrin, ta karyata dukka tuhume-tuhumen da ake mata a zaman baya.

An gurfanar da wadanda ake zargin a babbar kotu ta shida da ke jihar a gaban Alkali Usman Na-Abba.

Kisan Hanifa: Abin da ya sa Gwamnatin Kano ta ba Abdulmalik Tanko aron Lauya a kotu

A gefe guda, mun ji cewa, Abba Hikima, wani Lauya mai kare hakkin al’umma a jihar Kano ya fitar da mutane daga duhu a game da lamarin shari’ar kisan Hanifa Abubakar.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun kashe mutane takwas, sun kona wani kauye a Borno

Barista Abba Hikima ya yi karin haske ne bayan ya ji mutane da-dama sun fito su na korafi a dalilin ba Abdulmalik Tanko lauya da gwamnatin Kano ta yi.

A shafinsa na Facebook, Hikima ya ce akwai dalilin da ya sa aka ga an dauki wannan matakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng