Duk za mu mutu: Yaro ya fashe da kuka, yana tsoron ka da Rasha ta harbo bam Najeriya
- Wani karamin yaro dan Najeriya ya bar mutane cikin mamaki da dariya bayan da aka gan shi yana sharbar kuka saboda mamayar da Rasha ke ci gaba da yi a Ukraine
- A lokacin da wata mata ta tambaye shi, yaron ya bayyana fargabar cewa Rasha za ta aika bama-bamai domin hallaka kowa a fadin Najeriya
- Amsar da ya bayar ta ba matar da mamaki amma yaron ya tsaya tsayin daka cewa ba ya son ya mutu a irin wannan yanayi na yaki
Najeriya - Yayin da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ke ci gaba da samun tofin Allah tsine a duniya daga shugabannin duniya, wani karamin yaro ya shiga cikin rudani yayin da ya bayyana fargabar abin da yake tunani.
Tashin hankali: Wani mutum ya daba wa mahaifiyarsa wuka har lahira yayin da yake fada da matarsa a Neja
A ranar 24 ga watan Fabrairu, shugaban kasar Rasha ya ba da sanarwar kaddamar da farmakin soji a yankin Donbas na gabashin Ukraine, matakin da ya sa aka kakaba wa Rasha takunkumi daga kasashe daban-daban.
A wani sabon faifan bidiyo da @saintavenue_ent1 ya yada a Instagram, wata mata ta tambayi wani karamin yaro yayin da yake sharbar kuka.
Yaron ya ce yana sharbar kuka ne saboda tsoron rasa ransa domin kuwa Rasha ta aika bama-bamai domin lalata Najeriya, a fahimtarsa.
Cikin kuka ya ce idan Rasha ta yi haka babu wanda zai tsira a Najeriya har da shi kansa yaron.
A cewarsa:
“Idan (Rasha) suka aika bam zuwa Najeriya, yanzu dukkanmu za mu mutu.”
Da alamu dai bai fahimci ya lamarin yake ba, wannan yasa matar ta kyalkyale da dariya.
Kalli bidiyon:
Martanin 'yan soshiyal midiya
'Yan Najeriya sun mayar da martani game da bidiyon yaron, ga kadan daga ciki:
@e_smiler_ ya ce:
"Mutumin da bai taba sanin komai ba a rayuwa, da gaskiyarka bro."
@bdrickcool ne ya rubuta
"Ba ka so ka shiga aljanna ne kuma?"
@eniadefunkebu1 yayi sharhi da cewa:
"Haka ne, nima naji tsoro oo amma irin wannan ba zai faru ba a Nigeria da sunan Yesu, Amin."
Mun zo taya ku yakar Rasha: Dandazon 'yan Najeriya sun cika ofishin jakadancin Ukraine
A wani labarin, kimanin matasa 115 ‘yan Najeriya ne, a ranar Talata, 1 ga watan Maris, suka nuna sha'awar shiga yakin kasar Ukraine da Rasha.
Matasan da suka yiwa ofishin jakadancin Ukraine da ke Abuja babban birnin Najeriya kawanya, sun kuma sanya sunayensu a cikin wata rajista da ofishin jakadancin ya bayar.
Jaridar Guardian ta rawaito cewa jami'an ofishin jakadancin sun dakile yunkurin daukar hotunan mutane a bakin ofishin.
Asali: Legit.ng