Gwamnan Abia zai biya diyyan N2m ga iyalan Hausawan da aka kashe a kasuwar dabbobi

Gwamnan Abia zai biya diyyan N2m ga iyalan Hausawan da aka kashe a kasuwar dabbobi

  • Gwamnatin jihar Abia ta yi takakkiya zuwa Gombe don jajantawa gwamnatin jihar bisa abinda ya auku kwanakin baya
  • Wasu yan bindiga sun far wa Hausawa yan kasuwar dabbobi da rana tsaka bai gaira ba dalili
  • Tuni gwamnati, kungiyoyin kare hakkin bil adam da masu sharhi kan lamura yau da kullum sukayi tirr da wannan abu

Mukaddashin shugaban kungiyar dilolin dabbobin Najeriya, Yahuza Yusuf, ya bayyana cewa Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya yi alkawarin biyan kudin diyyan N2m ga iyalan kowani mutum guda cikin wadanda aka kashe a kasuwar dabbobi a jihar.

Yahuza, ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayinda wakilan gwamnatin jihar Abia karkashin Sarkin masarautar Abiriba, Kalu Ogbu, suka ziyarci gidan gwamnatin jihar Gombe, rahoton Cable.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna

Mafi akasarin Hausawan da aka kashe a harin yan asalin jihar Gombe ne.

Mataimakin Gwamnan Gombe, Manasseh Danile Jatau, ne ya karbi bakuncin tawagar gwamnatin Abia.

Kasuwar dabbobi
Gwamnan Abia zai biya diyyan N2m ga iyalan Hausawan da aka kashe a kasuwar dabbobi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Jack Tasha, a jawabin da ya saki ya ruwaito Yahuza da cewa gwamnan na Abia ya biya N150,000 matsayin diyyar kowani shanu guda da aka kashe.

A cewarsa:

"Yace, gwamnatin ya rage radadin harin ta hanyar biyan N150,000 (Dubu dari da hamsin) kan kowani Shanu guda da aka kashe kuma ya yi alkawarin biyan N2,000,000 (Milyan biyu) matsayin diyya ga iyalan mamatan,"

A nasa jawabin, mataimakin gwamnan Gombe, ya jinjinawa gwamnatin Abia bisa daukar wannan mataki da jajantawa jihar don karfafa alaka tsakanin Arewa da Kudu.

Ba Inyamurai suka kashe yan Arewa a Abia ba, kuyi hakuri: Ohanaeze ga al'ummar Arewa

Kara karanta wannan

Ina tare da dalibai mata Musulmai, babu wanda ya isa ya hanasu sanya Hijabi: Gwamnan Kwara

A baya, kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta jajantawa al'ummar Arewa, Malaman addinin, Sarakunan gargajiyan Arewa, da kungiyar dattawan Arewa bisa kisan Hausawa a jihar Abia.

A jawabin da sakatare janar na kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro, ya baiwa manema labarai a Kaduna, yace suna aika sakon ta'aiyya ga shugabannin arewa da wadanda sukayi rashin 'yanuwansu a abinda ya faru a Abia.

Kungiyar ta bayyana cewa ba yan kabilar Igbo bane, wau yan bakin haure ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng