‘Ƴan Daba’ Sun Sake Banka Wa Wata Ofishin Ƴan Sanda Wuta

‘Ƴan Daba’ Sun Sake Banka Wa Wata Ofishin Ƴan Sanda Wuta

  • Wasu batagari sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda da ke Okwelle a karamar hukumar Onuimo a Jihar Imo inda suka je da bindiga suka dinga harbe-harbe
  • Bayanai sun nuna yadda ‘yan bindigan suka yi dirar-mikiya a ofishin ‘yan sandan da tsakar dare a lokacin babu wani dan sanda da ke kan aiki
  • Wannan farmakin ya biyo bayan wani harin wanda ‘yan bindiga suka tayar da wani ofishin ‘yan sanda da ke Isa har suka halaka wasu ‘yan sanda guda biyu

Jihar Imo - Wasu ‘yan bindiga sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Okwelle da ke cikin karamar hukumar Onuima a Jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito.

Wakilin Daily Trust ya bayyana yadda ‘yan bindigan suka isa ofishin da tsakar dare suka dinga harbe-harbe, sai dai babu wani dan sanda da ke kan aiki a ranar.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

‘Ƴan Daba’ Sun Sake Banka Wa Wata Ofishin Ƴan Sanda Wuta
Batagari Sun Sake Banka Wa Wata Ofishin Ƴan Sanda Wuta Imo. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Harin ya biyo bayan makwanni kadan da ‘yan bindigan suka kai farmaki ofishin ‘yan sanda na Isu har suka halaka ‘yan sanda biyu da ke bakin aiki.

Dama wannan ne kadai ofishin ‘yan sanda da ke yankin, kuma sun kona shi

Wani ganau wanda ya bukaci a boye sunan sa ya ce ‘yan sandan suna tafiya ne wani ofishin na daban da dare, sai da safe su kara bude wannan.

Kamar yadda ganau din ya shaida:

“Mun gano suna kwana ne a dayan ofishin. Daren da ya gabata bata-garin sun je ofishin inda suka banka wuta. Wannan ne kadai ofishin ‘yan sanda da ke aiki a yankin nan kuma sun babbaka shi.
“Wannan abu ne mara dadi.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya kara da cewa babu wanda ya mutu sakamakon harin.

Kara karanta wannan

Rasha ta fara kai hare-hare a Ukraine, ‘Daliban Najeriya 4, 000 sun yi carko-carko

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164