Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

  • Sufeta janar na 'yan sandan Najeriya ya bayyana damuwarsa kan yadda ake amfani da makamai ta haramtattun hanyoyi
  • Ya yi wannan korafi ne yayin da ya kai ziyarar aiki wani ofishin 'yan sanda da ke babban birnin tarayya Abuja
  • Ya kuma yi kira ga sauran hukumomin tsaro kan su kula wajen gudanar da ayyukan da suka shafi tsaron kasar nan

FCT, Abuja - Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba a ranar Talata ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda jami’an ‘yan sanda ke amfani da bindigogi ba ta hanyoyin da basu dace ba a fadin kasar nan.

Baba ya bayyana haka ne a wani rangadin kwana daya da ya kai a ofishin 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ango Abdullahi: Dalilin da yasa bana goyon bayan tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyi

Sufeto janar na 'yan sanda ya koka halin 'yan sanda
Yanzun nan: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya bukaci jami’an ‘yan sanda da kada su yi amfani da ikonsu ta hanyar sanya rayuwar 'yan Najeriya cikin wahala ba gaira ba dalili.

IGP din ya kuma shawarci hukumomin tsaro da su rungumi hadin kai domin samun sakamako mai kyau a yaki da miyagun laifuka a kasar.

Kotu ta yi watsi da bukatar Abba Kyari, ta ce ba za a bada belinsa ba

A bangare guda, rahotanni daga wata babbar kotun tarayya da ke Abuja sun ce, kotun ta ki bayar da belin DCP Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar (DCP) bisa wasu tuhume-tuhume.

The Cable ta ruwaito cewa, mai shari'a Inyang Ekwo, ya yanke hukunci a ranar Litinin, cewa bukatun da aka bijiro dasu sun wuce gona da iri.

Kara karanta wannan

Abuja: 'Yan bindiga sun hallaka 'yan mata biyu a hanyarsu ta zuwa biki

Idan baku manta ba, a ranar 14 ga Fabrairu, hukumar NDLEA ta bayyana cewa ana neman Kyari bisa “hannu a harkallar hodar iblis mai nauyin kilogiram 25”.

Sa’o’i kadan bayan haka, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da kama shi tare da mika shi ga hannun hukumar NDLEA.

Kotu ta amincewa NDLEA ta ci gaba da tsare Abba Kyari da abokan harkallarsa 6

A wani labarin, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar hukumar NDLEA na neman izinin ci gaba da tsare Abba Kyari da wasu mutum shida da ake zargi da harkallar miyagun kwayoyi tare da Abba Kyari.

Mai shari’a Zainab Abubakar ta bayar da umarnin a tsare Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus na tsawon kwanaki 14 a cibiyar NDLEA da ke Abuja kafin a gudanar da bincike, inji rahoton The Nation.

Rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa, ci gaba da tsare Abba Kyari da 'yan tawagarsa zai ba hukumar ta NDLEA damar ci gaba da bincike mai zurfi kan lamarinsa, kamar yadda lauyan NDLEA ya nema.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta yi watsi da bukatar Abba Kyari, ta ce ba za a bada belinsa ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.