Air Peace vs Sarkin Kano: Muna baiwa kwastmominmu hakuri amma ba laifinmu bane
- Karo na biyu, kamfanin Air Peace ya sake martani ga masarautar Kano bisa abinda ya faru makon da ya gabata
- Masarautar dai ta bukaci kamfanin ya baiwa mai martaba Sarki hakuri bisa kin jinkirta tashin jirgi
- Air Peace ya baiwa daukacin kwastamominsa hakuri bisa abinda ya faru
Legas - Shugabannin kamfanin Air Peace sun yi martani ga masarautar Kano cewa su suka jinkirta jirginsa na Banjul, Gambia zuwa Legas makon da ya gabata.
A jawabin da kamfanin ya daura a shafinsa na yanar gizo ranar Lahadi, ya bayyana cewa jirgin Banjul zuwa Legas mai zaman kansa ne, ba shi da alaka da jirgin Legas-Kano.
Air Peace ya saki jawabin ne matsayin martani ga bukatar masarautar Kano na a baiwa Sarki hakuri cikin kwanaki uku.
Jawabin yace:
"Bisa jita-jitan dake yawo a kafafen yada labarai cewa jirgin Banjul-Legas na ranar 24 ga Febrairu, 2022, wanda ke dauke da Sarkin Kano, muna son bayyanawa duniya cewa jirgin mai zaman kansa ne."
"Jirgin iyakar tafiyarsa Legas kuma bai da alaka da wani waje, saboda haka, kamfanin ba zai san manufar fasinjojinsa ba."
"Amma muna baiwa kwastamominmu hakuri da suka gaza isa inda suka nufa kamar yadda suka so."
Air Peace dai bai yi magana kan hakurin da masarautar Kano ta bukata ba.
Masarautar Kano ta baiwa kamfanin Air Peace kwanaki 3 ta baiwa Sarkin Kano Hakuri
Shugaban tsare-tsare na masarautar Kano, Isah Bayero, ya baiwa Air Peace sa'o'i 72 su baiwa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, hakuri bisa wulakantashi da suka yi da jinkirta tafiyarsa.
Yace wajibi ne kamfanin Air Peace ya amsa cewa yayi laifi wajen kin bin tsari, wanda haka ya sabbaba jinkirin Sarkin Kano a tashar jirgin Legas.
A cewarsa,
"Tun da sun jinkirta tashinmu daga Banjul, wanda ya sabbaba jinkirin zuwa Legas, ya kamata Air Peace ya shirya yadda za'a damu. Amma babu abinda sukayi."
"Ina basu sa'o'i 72 su baiwa Sarki hakuri, na farko a jarida, na biyu kuma su turo wakilai wajen Sarki. Babu abinda ba zamu iya yi don kare mutunci masarautarmu ba."
Asali: Legit.ng