Kano: Kotu ta aike mutumin da aka kama da sunki 39 na wiwi gidan gyaran hali

Kano: Kotu ta aike mutumin da aka kama da sunki 39 na wiwi gidan gyaran hali

  • Kotun shari'a da ke zama a Fagge ta jihar Kano ta aika matashi mai shekaru 25 mai suna Ibrahim Shehu zuwa gidan yari
  • An kama Ibrahim Shehu da sunki 39 na tabar wiwi a kwatas din Kwana Hudu da ke kwaryar birnin Kano yayin sintiri
  • Duk da Ibrahim ya amsa laifinsa, alkali Bello Khalid ya bayar da umarnin tsare shi a gidan yari har zuwa watan Maris

Kano - Wata kotun shari'a da ke zama a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano ta aike matashi mai shekaru 25 mai suna Ibrahim Shehu kan zarginsa da mallakar sunki 39 na busasshen ganye da ake zargin tabar wiwi ce.

Wanda ake zargin mazaunin Kwana Hudu ne a birnin Kano kuma yana fuskantar zargin laifin mallakar busasshen ganyen tabar wiwi, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Alkali ya bada umarni hukumar EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamnan APC a Abuja

Kano: Kotu ta aike mutumin da aka kama da sunki 39 na wiwi gidan gyaran hali
Kano: Kotu ta aike mutumin da aka kama da sunki 39 na wiwi gidan gyaran hali. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: Facebook

Duk da wanda ake zargin ya amsa cewa ya aikata laifin, alkali Bello Khalid ya bada umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali.

Tun farko dai, lauyan masu gurfanarwa, Abdul Wada, ya sanar da kotun cewa wanda ake zargin an kama shi ne a kwatas ta Kwana Hudu da ke Kano yayin sintiri.

Ya ce a wannan ranar wurin karfe 8 na yamma, an kama wanda ake zargin da sunki 39 na busasshen ganye wanda ake zargin tabar wiwi ce.

Daily Trust ta ruwaito cewa, mai gurfanarwan ya ce wannan laifin ya ci karo da sashi na 137 na dokokin shari'a na jihar Kano.

Alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Maris domin yanke hukunci.

NDLEA ta kwace kwayoyin Tramadol 649,300 a filin jirgin sama na Legas

Kara karanta wannan

Kotu ta sake umartar 'yan sanda su kamo Jaruma mai sayar da kayan-mata

A wani labari na daban, jami'an hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) sun kama a kalla kwayoyin Tramadol masu nauyin 225mg guda 649,300 da Euro809,850 da sauran miyagun kwayoyi da aka shigo dasu daga Pakistan, Australia da Italiya a titin jirgin Murtala Muhammad (MMIA) na Ikeja dake jihar Legas.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce, a ranar Lahadi a Abuja, jami'an hukumar sun kara kama sauran miyagun kwayoyin da aka shigo dasu daga Turai, America da Canada a wannan filin jirgin.

Kamar yadda ya bayyana, a kamfanin kula da sufirin jiragen sama na Skyway, ma'aikatan hukumar sun kwace kwayoyin Tramadol na 225mg guda 549,300 masu nauyin kilo 460.95 wanda aka shigo dasu daga Pakistan ta Addis Ababa ta jirgin Ethiopia a ranar 16 ga watan Fabrairu, tare da kama wani wanda ake zargi, Nwadu Ekene Christian.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng