Wasu yan Najeriyan da muke kokarin kwasowa daga Ukraine sun ce ba zasu dawo ba, Minista waje

Wasu yan Najeriyan da muke kokarin kwasowa daga Ukraine sun ce ba zasu dawo ba, Minista waje

  • Yayinda gwamnati tayi alkawarin fara kwashe yan Najeriya daga Ukraniya ranar Laraba, wasu sunce ba zasu dawo ba
  • Kimanin yan Najeriya 12,000 wanda da ya hada da mazauna da dalibai aka kiyasta suna kasar Ukraniya
  • Gwamnatin tarayya tace nan da ranar Laraba za'a tura jirage kwaso yan Najeriyan da suka samu damar tsallakawa

Abuja - Wasu yan Najeriyan da suka makale a Ukraine sakamakon yakin kasar da kasar Rasha basu da niyyar dawowa gida.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyema, ya bayyana hakan lokacin da ya gana da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ranar Litinin, rahoton DailyTrust.

Yace:
"Muna kyautata zaton karar kwasosu ranar Laraba duk da cewa wasu basu son dawowa."
"Muna iyakan kokarin ganin cewa nan da Laraba zamu tura jirage kwaso su."

Kara karanta wannan

Ango Abdullahi: Dalilin da yasa bana goyon bayan tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyi

Onyeama ya kara da cewa kawo yanzu an baiwa yan Najeriyan da suka gudu wasu kasashe daga Ukraniya masauki da abinci kafin a dawo da su Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Minista waje
Wasu yan Najeriyan da muke kokarin kwasowa daga Ukraine sun ce ba zasu dawo ba, Minista waje
Asali: Facebook

Gwanda mu mutu da mu koma Najeriya, Wasu yan Najeriyan dake kasar Ukraniya

Wasu yan Najeriya dake zaune kasar Ukraniya yanzu haka sun yi watsi da maganar gwamnatin tarayya na kwasosu daga can sakamakon yakin kasar da Rasha

Daily Trust ta ruwaito wasu yan Najeriya na cewa sun gwammace yaki ta ci su da su dawo gida Najeriya.

Treasure Chinenye Bellgam, wani dalibi ya ce abinda gwamnatin Najeriya ke kokarin yi na da kyau amma,

"Mafi akasarin yan Najeriya kudi suka zo nema kuma ba zasu yarda su koma Najeriya ba, sun gwammace su mutu a nan."
"Kamar Allah ya daga ka ne amma kana son komawa baya, kamar koma baya (komawa Najeriya)."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Hukumar FIFA da UEFA sun cire Rasha daga cikin duniyar kwallo

Wani matashin Julius yace gaskiya yan Najeriya ba zasu yarda su koma gida ba.

Yace:

"Dubi ga yadda tattalin arzikin Najeriya yake, ina ga yawancin mutane zasu nemi wajen fakewa ne amma ba komawa Najeriya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng