Rikicin Masarautar Kano da Kamfanin jirgi: Ya kamata manya su saka baki, inji wata kungiya
- Kungiyar matasan arewa ta AYCF ta magantu a kan takaddama tsakanin kamfanin jirgin sama na Air Peace da masarautar Kano
- Shugaban kungiyar, Yerima Shettima ya bayyana cewa lamarin ya ki ci yaki cinyewa saboda manyan masu fada aji sun ki mayar da hankali a kai balle su yi sulhu
- Tun farko dai masarautar Kano ta zargi kamfanin jirgin da wulakanta sarkinta bayan sun ki jinkirta tashi daga Lagas zuwa Kano
Kungiyar matasan arewa ta nuna damuwarta a kan rashin jituwar da ke tsakanin masarautar Kano da kamfanin Air Peace yayin da ta yi kira ga manyan yan Najeriya da su shiga lamarin.
Shugaban kungiyar Alhaji Yerima Shettima ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ya bayyana cewa abun damuwa ne yadda aka gaza magance rashin jituwar da ke gudana a yanzu saboda dattawan kasar sun ki mayar da hankali kan haka ko kuma su yi wani yunkuri don ganin an samu zaman lafiya.
Mun ji cewa Yarima Isa Bayero, shugaban tsare-tsare na Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya zargi kamfanin jirgin da wulakanta sarkin ta hanyar kin jinkirta tashin jirginsa na Lagas zuwa Kano bayan ya jinkirta tashinsa daga Banjul, kasar Gambia zuwa Lagas.
Sai dai kamfanin jirgin ya karyata batun wulakanta sarkin sannan ya ce ya gwammaci ya kare martabarsa ta hanyar kin jinkirta tashi wanda an riga an kammala tsare-tsare.
Isa Bayero ya kuma ba kamfanin awanni 72 ya ba sarkin da mutanen masarautar hakuri a ranar Asabar.
Shugaban kamfanin Air Peace mutum ne mai mutunta sarakunan arewa - Yerima
Sai dai, kungiyar ta AYCF ta nuna kaduwa cewa an alakanta shugaban kamfanin Air Peace, Mista Allen Onyema, da rashin mutunta sarkin Kano, cewa shi Onyema da ya sani mutum ne da bai taba wulakanta wani sarki a arewa ba balle a kai ga sarkin Kano.
Ya ce ya zama dole manyan yan Najeriya masu fada aji su gaggauta shiga tsakanin ofishin daraktan shugaban tsare-tsaren na masarautar Kano da hukumar kamfanin Air Peace domin a samu zaman lafiya mai dorewa.
Ya ce basa so Kano, cibiyar hada-hadar kudi ta Arewa ta samu karancin kamfanonin jiragen kasuwanci da ke zirga-zirga a jihar, rahoton Vanguard.
Ta wani dalili zamu jinkirta jirgin da ya fara tafiya saboda mutum 1, Air Peace ya yi raddi
A baya mun ji cewa kamfanin jirgin sama na Air Peace, ya bayyana cewa ko kadan bai ci mutuncin mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ba.
2023: Magoya Bayan Yahaya Bello Sun Yi Wa Ganduje Zazzafan Martani Kan Cewa Arewa Na Goyon Bayan Tinubu, Sun Ce Ya Riƙe Girmansa
Shugabar harkokin ayyyukan kamfanin, Toyin Olajide, a jawabin da ta saki ta bayyana cewa karya Isa Bayero ya sharara saboda kamfanin Air Peace na ganin girman Sarkin Kano matuka.
A cewarta, sabanin abinda ake yadawa na cewa kamfanin ya ci mutuncin Sarkin, kare mutuncin Sarkin akayi.
Asali: Legit.ng