Kyawawan hotunan 'yar takarar gwamnan Kogi yayin da za ta amarce da rabin ranta, ta sanar da ranar biki
- Kyakyawar 'yar siyasa da ta taba fitowa takarar kujerar gwamnan jihar Kogi, Natasha Akpoti, za ta amarce da rabin ran ta
- Ta wallafa hoton ta tare da basaraken da za ta aura inda ta ce lokaci ya zo kuma a zo a taya su murna a ranar Asabar mai zuwa
- A sanarwar da ta wallafa, an ganta sanye da kayan al'ada tare da masoyinta inda suke kallon juna cike da shaukin so
Fitacciyar 'yar siyasar nan ta jihar Kogi, Natasha Akpoti ta shirya tsaf domin amarcewa da masoyinta, Emmanuel Uduaghan.
A wata wallafa a shafinta na Instagram da ta fitar, tsohuwar 'yar takara gwamnan jihar Kogin ta bayyana cewa za a yi aurenta a ranar 5 ga watan Maris a jihar Kogi.
Kamar yadda wallafar tace:
2023: Buhari Ya Gaza, Tsari Na Zai Banbanta Da Nasa Idan An Zaɓe Ni Shugaban Ƙasa, Ƴar Takara Mai Shekara 102
"Ga mu nan!!! Mun saje cikin al'ada... Cike da albarkar soyayya. Tabbas Ubangiji ne ke kyautata lamurran a lokacin da ya so.
"Ku zo ku taya mu shagali a ranar Asabar, 5 ga watan Maris ta 2022. Karfe 10 a plot 101 Dr. Jimoh Akpoti str. Obeiba-Ihima da ke karaamar hukumaar Okehi ta jihar Kogi.
"Mai martaba Chief Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan, Alema na masarautar Warri da Natasha Akpoti''
Kotun koli ta ba Bello da Jam’iyyar APC gaskiya a zaben Kogi
A wani labari na daban, kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar da Alhaji Yahaya Bello ya samu a matsayin zababben gwamnan jihar Kogi.
A wani hukunci da kotun koli ta zartar a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2020, an yi fatali da karar ‘yar takarar SDP, Natasha Akpoti.
Natasha Akpoti ta roki babban kotun kasar ta soke zaben da ya ba APC nasaara. Alkalai sun ce babu dalilin gabatar da wannan kara. Jaridar The Nation ta ce kotun koli a karkashin jagorancin mai shari’a, Ibrahim Muhammad ta yi watsi da hujjojin ‘yar takarar.
Asali: Legit.ng