Yanzu nan: Kotun koli ta ba Bello da Jam’iyyar APC gaskiya a zaben Kogi
Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar da Alhaji Yahaya Bello ya samu a matsayin zababben gwamnan jihar Kogi.
A wani hukunci da kotun koli ta zartar a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2020, an yi fatali da karar ‘yar takarar SDP, Natasha Akpoti.
Natasha Akpoti ta roki babban kotun kasar ta soke zaben da ya ba APC nasaara. Alkalai sun ce babu dalilin gabatar da wannan kara.
Jaridar The Nation ta ce kotun koli a karkashin jagorancin mai shari’a, Ibrahim Muhammad ta yi watsi da hujjojin ‘yar takarar.
‘Yar takarar jam’iyyar hamayya ta na tuhumar hukumar INEC da APC da ‘dan takararta cewa ba su lashe zaben da aka yi a Nuwamban 2019 ba.
SDP ta na karar an tafka magudi a zaben gwamnan Kogi, sannan ta ce Yahaya Bello da APC ba su samu kuri’ar da ta fi ta kowa yawa ba.
KU KARANTA: APC ta samu kuri'a 406, 00, PDP ta na da 189, 000 a zaben Kogi
Bayan haka kotun ta yi watsi da hujjojin da Injiniya Musa Wada da jam’iyyar PDP su ka gabatar, Alkalai sun ce babu dalilin a damu shari'a.
Alkalan kotun koli sun ce lauyoyin jam’iyyar adawar ba su iya gamsar da kuliya cewa an yi murdiya a zaben gwamnan jihar Kogi ba,
Alkalan babban kotun kasar da su ka saurari shari’ar sun hada da mai girma Alkalin Alkalan Najeriya, CJN Tanko Muhammad.
Sauran Alkalan da su ka zartar da wanan hukunci su ne: Olabode Rhodes-Vivour, Sylvester Ngwuta, da Inyang Okoro.
Akwai mata biyu a jerin Alkalan da su ka cin ma wannan hukunci, su ne: Amina Augie, Kudirat Kekere-Ekun, da Uwani Abba-Aji.
Bello mai shekara 45 ya samu kuri’a fiye da 406,000 a zaben da ya gabata. Wada shi ne ya zo na biyu, ya tashi da kuri’u 189, 704.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng