Matsafa sun yi luguden wuta kan masu makoki, sun yi fatali gawar mamacin
- Wasu miyagu da ake zargin matsafaa ne sun kutsa yankin Ebenebe da ke karamar hukumar Awka ta arewa ana tsaka da makoki
- Matsafan sun budewa jama'a wuta inda suka halaka jama'a masu yawa tare da yin fatali da gawar a wulakance a kasa
- Ana zargin dan kungiyar asiri ne ya rasu, hakan yasa kungiyar asiri ta adawa suka kutsa wurin makokin domin tozarta gawarsa
Anambra - Tashin hankali da hargitsi ya barke a Ebenebe da ke karamar hukumar Awka ta arewa da ke jihar Anambra a ranar Asabar yayin da wasu da ake zargin matsafa ne suka kutsa wurin makoki tare da halaka jama'a.
Daily Trust ta ruwaito cewa, 'yan bindigan sun tsinkayi wurin ne daidai lokacin da aka fito da gawar farfajiyar gidan mamacin.
A wani bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, an ga jama'ar yankin suna ihu da wayyo yayin da aka yi watsi da gawar a farfajiyar
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya tabbataar da aukuwar lamarin inda yace wasu matsafa ne suka shiga wurin makokin, Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Tabbas, a safiyar Asabar ne aka samu aukuwar lamarin a Ebenebe. Ana tsaka da makoki yayin da wasu da ake zargin maatsafa ne suka kutsa yankin taare da fara harbe-harbe," yace.
Kamar yadda Ikenga yace, binciken farko ya bayyana cewa ana birne wani dan kungiyar asiri ne yayin da wata kungiyar asiri ta adawa suka shiga wurin tare da fara harbin mutane.
Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Echeng Echeng ya yi umarnin tura 'yan sanda yankin domin kwantar da tarzomar.
"Ba mu san hakikanin yawan wadanda aka halaka ba, amma zan sanar da ku matukar muka samu karin bayani. A yanzu kwamishinan 'yan sanda Echeng Echeng ya aika da 'yan sanda yankin domin kwantar da tarzomar," yace.
Wannan al'amarin na faruwa ne a yayin da hare-hare suka yawaita a yankin kudu maso gabas.
'Yan bindiga sun bude wa masu saka kuri'a wuta, sun halaka 5
A wani labari na daban, Kimanin mutane biyar sun rasa rayukan su a lokacin da 'yan bindiga suka kai farmaki a wuraren zabe guda biyu yayin gudanar da zaben karamar hukumar jihar Enugu a ranar Laraba.
'Yan bindigan sun auka wa akwatin zabe a gunduma ta uku dake karamar hukumar Enugu ta kudu da wani akwatin zaben dake Akpugo cikin Nkanu dake karamar ta karamar hukumar ta yamma, Daily Trust ta ruwaito.
'Yan bindigan sun hargitsa wurin, ta hanyar lalata kayayyakin zabe bayan fattatakar masu zaben.
Bayan halaka matanen da suka yi, wasu sun samu raunuka, yayin da suka bankawa ababen hawa wuta, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng