Yanzu Haka: Atiku Ya Kai Wa Obasanjo Ziyara a Gida, Sun Keɓe Suna Ganawar Sirri
- A ranar Asabar mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya isa gidan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta a Jihar Ogun
- Ya kai ziyarar ne da misalin karfe 10 na safe inda suka fara ganawar sirri saboda shirin sa na fitowa takarar shugaban kasa kamar yadda ya yi a shekarar 2019
- Duk da dai har yanzu Atiku bai sanar da kudirinsa na takarar ba, amma ya fara bibiyar manyan mutane inda yake neman goyon bayan su a wurare daban-daban cikin kasar nan
Ogun - Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya kai ziyara har gidan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo don tattaunawa da shi akan burin sa na takara, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kai ziyarar ne har gidan Obasanjo da ke Abeokuta cikin Jihar Ogun a ranar Asabar da safe inda ya nufi penthouse da ke cikin Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) a Abeokuta da misalin karfe 10 na safe inda suka shiga ganawar sirri da Obasanjo.
Atiku yana ta kamfen
Har yanzu Atiku bai riga ya bayyana burinsa na takara ba amma tuni ya fara kamfen inda ya ke ta zuwa wurare daban-daban yana neman goyon baya.
Lokacin da ya kai wa Raymond Dokpesi, tsohon shugaban Daar Communications, ziyara a Jihar Abia wanda shi ne gaba-gaba a mara wa Atiku baya, cikin watan da ya gabata, ya ce in har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, sau daya kawai zai yi mulki.
Dokpesi ya ce Atiku ne dan takarar shugaban kasa mafi nagarta
A cewar Dokpesi:
“Atiku ne shugaban da ya fi dacewa da Najeriya. Amma a lokacin da zai hau zai cika shekaru 80. sai dai shi ne kadai zai iya ceto Najeriya a halin yanzu.
“Muna da kalubale masu tarin yawa a kasar nan. Da zarar an shirya shimfida mai kyau ga Najeriya, za a samu ci gaba. Ba zai zo mulki saboda yunwa ba sai don cika burin Najeriya.”
Atiku ne mataimakin Obasanjo lokacin da ya yi mulki a shekarra 1999 da 2007, kuma ya nemi takara a 2007, 2011 da 2019.
Ana sa ran Atiku da Obasanjo za su gana da wani basarake
Daily Trust ta ruwaito yadda Atiku ya samu rakiyar hadimansa zuwa Abeokuta a ranar Juma’a don samun damar kamfen din a ranar Asabar.
Ana sa ran Atiku da Obasanjo zasu samu ganawa da shugaban gargajiyar Egbaland, Oba Adedotun Gbadebo.
Asali: Legit.ng