Ganduje na da bayanai da yawa kansa na rashawa, Sakataren kwamitin yaki da cin hanci
- An shirya taron hanyoyin da za'a bi wajen magance cin hanci da rashawa a Najeriya a Abuja
- Yayin tattauna matsalolin rashawa a Najeriya sunan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya fado
- Babban 'dan gwamnan Kano ya yi barazanar shigar da mahaifinsa kotu kan wata sabuwar badakalar
Sakataren kwamitin yaki da rashawa na fadar Shugaban kasa (PACAC), Sadiq Radda, ya bayyana cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano na da tambayoyi da yawa da zai amsa kan zarge-zargen rashawa.
Sadiq Radda, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a taron yaki da rashawa na 26 da aka shirya a birnin tarayya Abuja, TheCable ta ruwaito.
Radda ya bayyana mamakin yadda 'dan Ganduje ya kai mahaifiyarsa kara wajen hukumar EFCC kan zargin damfara.
El-Rufai: Ni da wasu gwamnoni 5 za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don murkushe 'yan binidiga
Yace gwamnan na da tambayoyi da yawa da zai amsa tun yanzu da yake Ofis ballantana idan ya bar ofis.
A cewarsa:
"Kun ga a Kano, Ganduje na da bayanai da dama tun yanzu da yake Ofis, hakazalika zai yi bayani idan ya bar ofis kuma abin takaici karon farko a Najeriya 'da ya kai mahaifiyarsa kara wajen EFCC"
Shahrarren Lauya, Femi Falana, wanda yake taron ya bayyana cewa ikirarin yaki da rashawar da gwamnatin Buhari ke yi duk shadi fadi ne.
A cewarsa, ma'aikatar Shari'a ta gaza hukunta mutum daya da aka kama da rashawa, hakazalika tana hana kokarin tabbatar da adalci.
Bayan ya hada mahaifiyarsa da EFCC, Abdulaziz Ganduje ya na shirin kai mahaifinsa kotu
Babban yaron gwamnan jihar Kano, Abdulazeez Ganduje, yana barazanar yin shari’a da mahaifinsa, Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Jaridar Daily Nigerian ta ce Abdulazeez Ganduje yana yunkurin kai kara a kotu ne saboda gwamnatin mahaifinsa ta ki biyansa kudin kwangila.
Rahoton ya ce kamfanin Global Firm Nigeria Limited ya yi wa gwamnatin Kano aiki, amma Ganduje bai biya sa ragowar kudin aikinsa har N82m ba.
A cewar jaridar, a 2020 aka ba wannan kamfani na yaron gwamnan kwangilar maida cibiyar kula da ‘yan shaye-shaye ta Mariri ta zama makarantar IDP.
Asali: Legit.ng