Yanzu-yanzu: Jirgin haya yayi hadari a kasar Rasha, da dama sun mutu: Ma'aikatar tsaron Rasha
- Rikicin Rasha da Ukraine na cigaba da tsamari yayinda wani jirgin Rasha yayi hadari kusa da Kiev
- Kimanin yan Najeriya 12,000 wanda da ya hada da mazauna da dalibai aka kiyasta suna kasar Ukraniya
- Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana shirin kwaso yan Najeriya dake waje
Ma'aikatar tsaro kasar Rasha ya bayyana cewa wani jirgin haya ya yi hadari a cikin kasar Rasha kuma an yi asarar rayuka da dama.
Global Report ta ruwaito cewa jirgin mai dauke da mutum 26 ya fadi ne a yankin Voronezh kuma dukkan wadanda ke cikin sun mutu.
Dakarun Rasha sun hallaka Sojojinmu 137 daga fara yaki inji Shugaban kasar Ukraine
Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce akalla sojojinsa 137 aka hallaka a sakamakon barkowar da sojojin kasar Rasha suka yi masu.
Rahotanni daga jaridu da gidan talabijin na ketare irinsu NBC sun ce daga asubar jiya da sojojin Rasha suka shiga Ukraine zuwa yanzu, an rasa sojoji 137.
Baya ga haka, Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa sojojin kasarsa 316 sun samu rauni a hare-haren.
Volodymyr Zelensky ya bada wannan sanarwa da yake magana a shafinsa na Facebook, inda ya ce sauran kasashen Duniya su na tsoron taimakawa Ukraine.
Asali: Legit.ng