Na cire ɗana daga makarantar gwamnati ne saboda barazanar garkuwa da shi, Gwamna El-Rufa'i
- Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana cewa wasu sun fara kulla-kullan sace ɗansa shiyasa ya cire shi daga makaranta
- Gwamnan ya ce ba wai yana tsoron zasu samu nasara bane, baya son sauran dalibai rayuwar su ta shiga hatsari kan ɗansa
- A cewarsa, yana da kwarin guiwa kan ingancin ilimim makarantun gwamnati domin shi kansa ita ya yi
Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya ce ya zare ɗansa daga makarantar gwamnati ne saboda barazanar kai hari da garkuwa.
Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin sa ɗansa makarantar ne domin tabbatar da kwarin guiwarsa ga tsarin ilimin Kaduna, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Malam Nasiru ya yi wannan zancen ne a wurin taron manema labarai da ake shirya wa ministoci a fadar shugaban ƙasa dake Abuja, ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa shekaru biyar baya tun zuwansa kan mulki, gwamnatinsa ta ɗauki malaman makaranta fiye da adadin waɗan da ta kora daga aiki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan ya ce:
"Mun kori Malamai 22,000 kuma mun ɗauki 25,000. Mun gwada su lokuta da dama, wasu su faɗi kuma su sake faɗuwa, za mu kore su mu ɗauki wasu sabbi."
"Mun shirya inganta nagartan Malamai, saboda Malami shi ne ilimin ba wai ajin da ake zama ba. Yanzu zamu kawar da wasu malaman Sakandire."
"Amma mun ɗauki malaman da zasu koyar a Sakandire 7,700, muna jira ne mu kammala sallamar waɗan can. Kuma jami'an gwamnati mun cimma matsaya zamu saka 'ya'yan mu a makarantun gwamnati."
Meyasa gwamna ya cire ɗansa daga makaranta?
A cewar Elrufa'i a baya ya sanya ɗansa a makarantar gwamnati ne domin nuna wa al'umma ingancin ilimi karkashin gwamnatinsa.
"Na sa ɗana a makarantar gwamnati saboda ina da kwarin guiwa kan ingancin ilimin makarantun, wanda mu kan mu makarantar gwamnati muka yi."
"Amma ya zama wajibi na cire shi saboda wasu mutane na shirin kai hari na musamman domin sace shi. Bana tunanin za su yi nasara amma ina tsoron halin ɗa ƴaƴan talakawa za su shiga."
"Wannan dalilin ya sa na ga ya dace na cire shi, yanzu haka yana karatunsa a gida har zuwan lokacin da abubuwa za su yi kyau."
A wani labarin kuma mun kawo muku rahoton cewa Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna
Jami'in kwastam da yan bindiga suka bi har gida a Rigachikum, Kaduna suka bindige ya cika a Asibiti.
Maharan sun farmaki Mohammed Maradun, ɗan asalin jihar Zamfara a gidansa, Likitoci sun yi kokarin su amma rai ya yi halinsa.
Asali: Legit.ng