Cocin Anglican Ta Ba Wa Gwamna Zulum Na Jihar Borno Lambar Yabo

Cocin Anglican Ta Ba Wa Gwamna Zulum Na Jihar Borno Lambar Yabo

  • Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya samu lambar yabo daga cocin Anglican saboda kasancewar sa jajirtaccen shugaba a cikin lokacin nan mafi tsanani
  • Yayin ba shi lambar yabon a Port Harcourt, cikin Jihar Ribas, fiye da fastoci 600, cikin su akwai Archibishops guda 20, Bishops 144 da daruruwan rabaran duk sun taru
  • Babban rabaran na kasar nan, Dr. Henry Ndukuba ya mika lambar yabon ga shugaban ma’aikatan Jihar Borno, Barista Simon Malgwi wanda ya mika ta ga Gwamna Zulum

Rivers - Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya samu lambar yabo a matsayin sa na shugaba mafi jajircewa a matsanancin halin da kasa take ciki wanda cocin Anglican ta ba shi, The Punch ta ruwaito.

An yi taron karrama gwamnan ne a Port Harcourt, Jihar Ribas inda fiye da fastoci 600, ciki har da Archbishops guda 20, Bishops 144 da daruruwan rabaran.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan Bauchi ya kai wa Obasanjo ziyara har gida

Cocin Anglican Ta Ba Wa Gwamna Zulum Na Jihar Borno Lambar Yabo
Cocin Anglican Ta Karrama Gwamna Zulum na Jihar Borno. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban Cocin Anglican na Najeriya kuma Archbishop na gabadaya Najeriya, Rabaran Dr Henry Ndukuba ya mika lambar yabon ga shugaban ma’aikatan Jihar Borno, Barista Simon Malgwi, wanda ya mika lambar yabon ga Zulum a taron da aka yi a cocin St Andrews Anglican da ke Rumuobiokani a cikin Port Harcourt.

Bayar da lambar yabon ga Zulum shi ne makasudin shirya taron a wannan karon wanda su kan yi sau biyu a shekara kuma manyan Bishops da sauran wakilai na shiyyoyi 165 da ke cocin Najeriya duk sun halarta.

Babban musabbabin bayar da lambar yabon shi ne jajircewar Zulum akan jiharsa

Babban dalilin da ya sa aka karrama Zulum a cewar Ndukuba kamar yadda The Punch ta ruwaito, shi ne yadda gwamnan ya jajirce akan Jihar Borno cikin shekaru 3 ya yi ayyuka babu kakkautawa.

Kara karanta wannan

Mulki ba naku bane: Obasanjo ya shawarci tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023

A cewarsa:

“Wannan karramawar ba ta addini bace. Mun gaji da shugabannnin da suke yin son ran su haka yasa hadin gwiwar cocinan Anglican da ke Najeriya suka ga ka cancanci wannan karramawar sakamakon ayyukan da kake yi wa jama’a. Niyyar mu ita ce mu karrama shugaban da ya dage akan mutanen sa, hakan yasa muka ga kai ne ka dace.”

Ndukuba ya ci gaba da cewa:

“Farfesa Zulum shugaba ne na gari kuma muna alfahari da shi. An dade ana kai masa hari amma duk da haka bai dakata ba wurin yin ayyuka na gari ga jihar da ta kwashe shekaru 12 tana fama da rashin tsaro.
“Muna fatan Ubangiji ya yi maka jagora daga yanzu har gaba da abada.”

Zulum ya ce ya yi mamakin karramawar kasancewar shi ba kirista bane

A bangaren Zulum, ya yi godiya gare su inda yace ya yi mamamkin karramawar don bai taba zato ba.

Kara karanta wannan

Sakamakon zirga-zirgar Buhari: Kasar Ingila ta narka Naira Biliyan 5 domin inganta wuta

Kamar yadda yace:

“Na samu karramawa daga wurare daban-daban, amma wannan ta musamman ce saboda daga shugabannin addini tazo. Duk da ni ba kirista bane, hakan ya tabbatar da cewa da tsarkakakkiyar niyya kuka yi. Na gode kwarai.”

Wakilan da shugaban ma’aikatan Borno ya jagoranta sun hada da kwamishinan kawar da talauci, Mr Nuhu Clark, mai ba gwamna shawarwari na musamman akan harkokin jama’a, Mr Kester Ogualili da babban mai bayar da shawarwari ga gwamnan akan harkokin matasa da samar da ayyuka, Mr Christopher Akaba

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164