Jerin ayyuka 10 da gwamnatin tarayya za tayi da bashin $3bn da take shirin karba
Ministar kudi, kasafin kudi, da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin rattafa hannu kan sabon bashin $3.387 billion don yin wasu ayyuka 10 a fadin tarayya.
Ministar ta bayyana hakan a taron da ma'aikatar labarai da al'adu ta shirya kan nasarorin da Gwamnatin tarayya ta samu kan manyan ayyukan cigaba, rahoton Tribune.
Ga jerin ayyukan da tace za'ayi da kudin dan aka karbo bashin:
1. Layin dogon zamani na cikin birnin Kano (Aikin farko): US$673.2 million,
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Ginin titin Lafia By-Pass da fadada 9th Mile (Enugu)-Otukpo-Makurdi : US$845.75 million,
3. Samar da hanyar tsaron boda na zamani: US$175.5 million.
4. Aikin wutan lantarkin Najeriya (Off-Grid): US$350 million,
5. Aikin isar da lantarki (karkashin West African Power Pool): US$32.3 million,
6. Aikin wutan lantarki : US$486 million.
7. Aikin lantarkin dinke Najeriya: US$200 million,
8. Fadada hanyoyin raba wutan lantarki (karkashin Bankin cigaban Afrika AfDB): US$210 million
9. Shirin rabon wutan lantarkin birnin tarayya Abuja: US$170 million,
10. Aikin layin wutan lantarkin Arewa (Bankin cigaban Faransa): $245 million
Rashin wutan lantarki ya zama tarihi a Najeriya, Ministan Buhari
A bangare guda, karamin Ministan makamashin Najeriya, Goddy Jedy Agba, ya bayyanawa yan Najeriya cewa rashin wutan lantarki ya zama tarihi a kasar.
Agba yace nan da karshen shekarar nan, kashi 85% na yan Najeriya zasu samu lantarki a banza.
Ministan yace gwamnatin tarayya na kokari wajen ganin kowani gida a Najeriya ya samu mita.
Ya kara da cewa ayyukan lantarki da gwamnatin tarayya ta fara zasu kammala kafin karewar wa'adin shugaba Buhari.
Asali: Legit.ng