Da Dumi-Dumi: Gwamna Matawalle ya rantsar da sabon mataimakinsa, Sanata Nasiha

Da Dumi-Dumi: Gwamna Matawalle ya rantsar da sabon mataimakinsa, Sanata Nasiha

  • Gwamnan Zamfara ya rantsar da sabon mataimakinsa, Sanata Nasiha, jim kaɗan bayan tabbatar da shi da majalisar dokoki ta yi
  • Ya ce ya gaggauta daukar wannan matakin ne saboda dogon lokacin da aka ɗauka mataimaki baya halartar Ofis
  • Sanata Nasiha shi ne ɗan majalisa mai wakiltar Zamfara ta tsakiya, kuma tuni ya kama aiki a sabon ofishinsa

Zamfara - Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara ya rantsar da sabon Mataimakinsa, Sanata Hassan Nasiha.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan tsige tsohon mataimakin, Barista Aliyu Gusau, da kuma tantace sabon mataimakin da majaisar dokokin jihar ta gudanar yau Laraba.

Sanata Nasiha ya karbi shahadar fara aiki ne a wurin babbar alkalin jihar Zamfara, mai Shari'a Kulu Aliyu.

Kara karanta wannan

Zamfara: Bayan tsige mataimakin gwamna, majalisa ta maye gurbinsa da sanata

Matawalle ya rantsar da mataimakinsa
Da Dumi-Dumi: Gwamna Matawalle ya rantsar da sabon mataimakinsa, Sanata Nasiha Hoto: daily Nigerian/Facebook
Asali: Facebook

Babban mai taimakawa Matawalle ta bangaren labarai, Zailani Bappa, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar da yammacin Laraba.

Gwamnan ya ce matakin rantsar da sabon mataimakin cikin gaggawa ya zama wajibi duba da dogon lokacin da aka ɗauka Ofishin ba bu kowa.

Ya ce a yanzun ayyukan mataimakin gwamna da kundin mulki ya tanadar, za su cigaba da gudana kamar yadda ya kamata.

Bappa ya ce:

"Matawalle ya tuna wa mataimakin cewa ya zo a matsanancin lokaci da Zamfara ke bukatar sadaukarwa da kuma neman hanyoyin warware matsalar tsaro, da tattalin arziki."
"Ya kuma bukace shi ya yi amfani da karfin ikon da Kwansutushin ya ba shi wajen taimakawa gwamna sauke nauyin dake kansa."

Matawalle ya ƙara da cewa wajibi mataimaki ya zama mai gaskiya da biyayya, kuma bayan shawari da masu ruwa da tsaki ya zabi Sanata Nasiha saboda yana da duk abin da ake bukata.

Kara karanta wannan

Mahdi: Gaskiyar Abubuwa hudu da ya kamata ku sani game da Mataimakin Matawalle da aka tsige

Jawabin Sanata Nasiha

Da yake jawabin karban mukamin, mataimakin gwamnan ya jaddada goyon bayansa ga Matawalle da kuma gwamnatin jihar Zamfara.

Ya kuma bayyana cewa zai amfani da dukkan ƙarfinsa da dabarunsa wajen tabbatar da gwamnati da al'ummar jihar Zamfara sun samu nasara.

Kafin zama mataimakin gwamna, Nasiha shi ne Sanata mai wakiltar mazaɓar Zamfara ta tsakiya, kuma tuni ya kama aiki a sabon Ofishinsa.

A wani labarin kuma mun kawo muku cewa Kwamishinan gwamnan APC ya fice daga jam'iyya, ya koma PDP

Kwamishinan harkokin waje na jihar Imo da APC ke mulki, Fabian Ihekweme, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai hamayya.

Fitaccen ɗan siyasan ya jagorancin dandazon masoya da magoya bayansa a APC zuwa sabuwar jam'iyyar da ya koma PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262