Zamfara: Bayan tsige mataimakin gwamna, majalisa ta maye gurbinsa da sanata
- A yau ne majalisar dokokin jihar Zamfara ta tantance mutumin da zai maye gurbin mataimakin gwamna Aliyu Gusau
- An tsige Barista Aliyu Mahdi Gusau a yau dinnan, an kawo wanda zai maye gurbinsa nan take a majalisar dokoki
- Wannan na zuwa ne bayan da aka samu dambarwa tsakanin gwamnatin Zamfara da mataimakin gwamnan
Gusau, jihar Zamfara - A yau ne majalisar dokokin jihar Zamfara ta zabi Sanata Muhammad Hassan Nasiha a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar da ke Arewa maso Yamma, inji rahoton Channels Tv.
A zaman da aka yi yau, kakakin majalisar, Nasiru Mua’zu, ya karanta wasikar da gwamnan jihar Bello Matawalle ya aike masa na zabar Sanata Muhammad a matsayin mataimakin gwamnan jihar Zamfara.
An zabi Hassan ne sa’o’i bayan tsige Mahdi Gusau a yau Laraba. Sanata Hassan yana wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya, kamar yadda TheCable ta tattaro.
Dalilin zaban sabon mataimakin gwamna
An tsige tsohon mataimakin gwamna Gusau ne bayan da majalisar ta karbi rahoton kwamitin da babban alkalin jihar, Mai shari’a Kulu Aliyu ya kafa. Dama a baya an kafa kwamitin binciken zargin da ake yiwa mataimakin gwamnan.
Kwamitin mai mutane bakwai karkashin mai shari’a Halidu Soba mai ritaya ya mika rahotonsa majalisar dokokin jihar ne da ke Gusau babban birnin jihar.
A cewar wani mamba a kwamitin Oladipo Okpeseyi, kwamitin ya gudanar da aikinsa bisa gaskiya.
Kwamitin ya fara zamansa ne a ranar litinin kuma ya kammala zaman washegari. Amma Gusau wanda ake bincika bai halarci zaman binciken ba.
Wasu daga cikin zarge-zargen da ake masa sun hada da saba wa Kundin Tsarin Mulki, da rashin da’a, da zamba, da kuma cin zarafin mukaminsa.
Wannan lamari dai ya ba mutane da yawa mamaki, inda wasu ke ganin dole akwai wata maganar kasa.
Gwamnan Bauchi ya kai wa Obasanjo ziyara har gida
A wani labarin, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed a ranar Laraba ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Abeukuta, babban birnin jihar Ogun.
Mohammed ya na daya daga cikin masu hararo kujerar shugaban cin kasa a 2023 karkashin jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, Daily Trust ta ruwaito.
Tsohon ministan babban birnin tarayyan tare sa hadimansa sun isa gidan Obasanjo da ke dakin karatu na Olusegun Obasanjo a Abeokuta wurin karfe 11.30 na safe kuma kai tsaye suka shiga ganawar sirri ta tsawon sa'a daya da Obasanjo.
Asali: Legit.ng