Da Dumi-Dumi: Tashin Hankali yayin da Jirgin Sama makare da mutane ya yi gaggawar dira a Abuja

Da Dumi-Dumi: Tashin Hankali yayin da Jirgin Sama makare da mutane ya yi gaggawar dira a Abuja

  • Wani jirgin kamfanin Dana Air dake kan hanyar zuwa Legas makare da Fasinjoji ya yi saukar gaggawa a Abuja saboda dalilai
  • Matukin jirgin ya yi jawabi ga Fasinjojin da ya ɗakko mintuna kaɗan bayan sauka, ya ba su hakuri tare da gode musu da fahimtar lamarin
  • Tuni dai kamfanin ya samar da wani jirgi na daban, wanda ya kwashi Fasinjojin zuwa jihar Legas daga nan Abuja

Abuja - Wani jirgin sama na kamfanin Dana Air mai lamba 9J402 dake kan hanyar zuwa Legas ya yi saukar gaggawa a Abuja da misalin ƙarfe 2:25 na rana.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Jirgin ya samu wata matsala ne a sama wacce har yanzun ba'a bayyana ba, hakan ya sa ya yi gaggawar sauka ba tare da shiri ba.

Matukin Jirgin ya sanar ana tsaka da zuga tafiya a sama cewa akwai matsala kuma Jirgin ba zai iya cigaba da tafiya ba saboda wasu dalilai.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: Majalisar dokokin Zamfara ta tsige mataimakin gwamna daga kujerarsa

Dana Flight
Da Dumi-Dumi: Tashin Hankali yayin da Jirgin Sama makare da mutane ya yi gaggawar dira a Abuja Hoto: allafrica.com
Asali: UGC

Har yanzun da muke haɗa wannan rahoton, Fasinjoji na zaune a cikin jirgin suna jiran tsammanin kawo musu wani zaɓi don karasa tafiyar su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki kamfanin jiragen ya ɗauka?

Da yake jawabi ga Fasinjojin mintuna 25 bayan saukar da Jirgin, Matuƙin ya ce ya ɗauki wannan matakin saukar cikin gaggawa ne saboda tserar da rayuwarsu.

The Cable ta rahoto Ya ce:

"Bisa bai wa rayuwar Fasinjojin mu fifiko, mun dawo domin cika muku tafiyar ku. Muna godiya da fahimtar mu."

Bayan haka, Kamfanin jirgin ya juye Fasinjojin cikin jirgin da lamarin ya shafa a wani jirgi na daban, kuma tuni ya tashi zuwa jihar Legas.

A wani labarin kuma kun ji cewa Kwamishinan gwamnan APC ya fice daga jam'iyya, ya koma PDP

Kwamishinan harkokin waje na jihar Imo da APC ke mulki, Fabian Ihekweme, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai hamayya.

Kara karanta wannan

Bidiyon yaye dalibai: Lakcaran Abuja ya nade jamfarsa, ya tik rawa a wurin bikin yaye dalibai

Fitaccen ɗan siyasan ya jagorancin dandazon masoya da magoya bayansa a APC zuwa sabuwar jam'iyyar da ya koma PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262